Shugaban Nijar, Janar Adourahamane Tiani, ya jaddada muhimmancin haƙuri a ƙoƙarin tabbatar da ’yancin kan ƙasa, yana mai cewa dole ne a fara warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye ƙasar kafin a ga sakamako.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, Tiani ya ce:
“Rashin haƙuri dabi’ar mutane ce, amma idan ba ka warware abin da aka kulla ba, ƙoƙarinka zai tashi a banza.”
Ya ƙara da cewa: “Yaƙin da muke yi na tabbatar da ’yancin kanmu yana koya mana wannan a kullum. Muna ɗokin ganin an samu sakamako, amma da farko dole ne mu yi haƙuri wajen warware abubuwan da aka kullawa tsawon shekaru da dama.”
Sai dai Janar Tiani bai yi ƙarin bayani kan abin da ya sa ya wallafa saƙon ba, ko kuma takamaiman matsalolin da yake nufi.
Saƙon nasa ya zo ne a lokacin da Nijar ke fuskantar ƙalubale a fannoni daban-daban, ciki har da samar da mai da matsalar tsaro.
A makon da ya gabata, ƙarancin man fetur ya shafi birane da dama a ƙasar, ciki har da babban birnin Yamai, inda aka samu dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai.
Gwamnati ta ɗauki matakan wucin-gadi, ciki har da takaita sayar da mai da dare, domin sauƙaƙa jigila da sake cika tankunan gidajen mai. Rahotannin baya-bayan nan sun nuna cewa ana samun sauƙi a wasu wurare.
A ɓangaren tsaro kuma, an kashe aƙalla mutum 11 a harin da wasu masu ɗauke da makamai suka kai kan motocin bas biyu a hanyar Arlit zuwa Agadez da ke arewacin ƙasar a ranar 20 ga Oktoba. Rahotanni sun ce wasu mutane da dama sun jikkata a harin.
Nijar dai na ci gaba da fuskantar barazanar tsaro a wasu yankunanta, yayin da gwamnatin soji ƙarƙashin jagorancin Tiani ke jaddada ƙudurin ƙasar na tabbatar da cikakken ’yancin kanta da ikon tafiyar da al’amuranta.
Sai dai ba a bayyana ko saƙon shugaban na da alaƙa kai tsaye da waɗannan ƙalubalen ba.













