Ɗanwasan gaba na Bayern Munich da Ingila, Harry Kane, ya lashe kyautar Ballon d’Or ta maza ta shekarar 2026 a ranar Litinin, inda ya zama ɗanƙwallo na farko ɗan ƙasar Ingila da ya karɓi kyauta mafi daraja a fannin ƙwallon ƙafa a duniya tun bayan Michael Owen a shekarar 2001.
‘Yarwasan Spain Alexia Putellas ta samu tata kyautar Ballon d’Or ta Mata karo na uku.
An gabatar da kyaututtukan ne a bikin ba da lambobin yabo na Ballon d’Or karo na 70 da aka gudanar a zauren London Palladium, wanda shi ne karo na farko da aka gudanar da wannan babban bikin a babban birnin ƙasar Ingila.
Kane, mai shekaru 33, ya lashe kyautar ne a karon farko bayan ya zura ƙwallaye 73 a wasanni 65 da ya buga wa Bayern Munich da Ingila a kakar wasa ta 2025/2026, ciki har da ƙwallaye 61 a wasanni 51 da ya buga wa ƙungiyar ta Jamus, wacce ta lashe kofi biyu a gida (gasar lig da kofin cikin gida).
Kyaftin ɗin na Ingila ya kuma zura ƙwallaye shida a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026, inda ya taimaka wa ƙasarsa ta zo ta uku.
Ɗanwasan gaba na Real Madrid da Faransa Kylian Mbappe ne ya zo na biyu a zaɓen Ballon d’Or na Maza, yayin da ɗanwasan Barcelona da Spain Lamine Yamal ya zo na uku.
Kane ya zama ɗanwasa na biyar ɗan ƙasar Ingila da ya lashe kyautar, inda ya shiga ya sahun su Stanley Matthews, Bobby Charlton, Kevin Keegan da kuma Owen, wanda shi ne ɗan Ingila na karshe da ya taba lashe kyautar a shekara ta 2001.
Ousmane Dembele na Paris Saint-Germain ne ya lashe kyautar a shekarar 2025.
A wani ɓangaren kuma, Putellas, mai shekaru 32, ta lashe kyautar Ballon d’Or ta Mata karo na uku bayan nasarorin da ta samu a shekarar 2021 da 2022, inda ta yi daidai da tsohuwar abokiyar wasanta a Barcelona, Aitana Bonmati.
‘Yarwasan tsakiyar ta ƙasar Spain ta jagoranci Barcelona zuwa lashe kofuna huɗu a jere a kakar wasa ta 2025-26, inda ta lashe La Liga F, Copa de la Reina, Super Cup ta Spain da Gasar Champions League ta Mata.
An kuma zaɓe ta a matsayin ‘yarwasan da ta fi kowa hazaƙa a Gasar Zakarun Turai sannan ta taimaka wa Spain lashe gasar Nations League ta Mata.
Putellas ta koma ƙungiyar London City Lionesses a watan Yuli bayan ta ci kofuna iri-iri a Barcelona.
Sauran wadanda suka lashe kyaututtuka su ne:
Ɗanwasan Barcelona da Spain, Lamine Yamal, ya lashe kyautar Kwararren Matashin Dan Wasa na Maza a karo na uku a jere, yayin da ‘yarwasan gaba ta Barcelona, Vicky Lopez, ta lashe kyautar ta mata a karo na biyu a jere.
Kocin Spain wanda ya lashe kofin duniya, Luis de la Fuente, an naɗa shi Kocin Maza na Shekara, yayin da Pere Romeu na Barcelona ya samu kyautar kocin mata.
Unai Simon na Athletic Bilbao ya lashe kyautar Gwarzon Gola na Maza na Shekara, yayin da Cata Coll ta Barcelona ta karbi kyautar a bangaren mata.
Kane na Bayern Munich ya kuma karbi kyautar Dan Wasan Gaba na Maza na Shekara biyo bayan kakar wasansa ta kwarewa, yayin da ‘yarwasan gaba ta Mexico, Charlyn Corral, ta zama ‘yarkasar Mexico ta farko da ta lashe kyautar ‘Yar Wasan Gaba ta Mata ta Shekara.
Barcelona ta samu kyautar Kungiyar Mata ta Shekara, yayin da Paris Saint-Germain (PSG) ta lashe kyautar kungiyar maza.














