| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
An kashe fararen-hula akalla 37 a wani harin kwanton-ɓauna a yammacin Jamhuriyar Nijar
Majiyoyin yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Juma’a cewa harin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, inda aka kai wa wasu mazauna kauyen Tillim hari a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako-mako a birnin Tera, d
An kashe fararen-hula akalla 37 a wani harin kwanton-ɓauna a yammacin Jamhuriyar Nijar
Daga cikin wadanda suka mutu akwai mambobin kungiyar sa-kai 11, mata bakwai da maza 20. / TRT Afrika Hausa

Akalla fararen-hula 37 ne suka mutu bayan wasu ‘yanbindiga sun kai musu harin kwanton-bauna a yammacin Nijar, kusa da iyakar kasar da Burkina Faso da Mali.

Majiyoyin yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Juma’a cewa harin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, inda aka kai wa wasu mazauna kauyen Tillim hari a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako-mako a birnin Tera, da ke yankin Tillaberi.

Wani tsohon zababben jami’in gwamnati ya ce wadanda abin ya shafa na tare da mambobin wata kungiyar sa-kai ta tsaron al'umma a lokacin da wasu ‘yanbindiga da ba a san ko su waye ba suka yi musu kwanton-bauna.

Ya ce mutane 37 sun mutu nan take, yayin da wani mutum kuma ya rasu daga baya sakamakon raunukan da ya samu a harin.

Daga cikin wadanda suka mutu akwai mambobin kungiyar sa-kai 11, mata bakwai da maza 20.

Wani mazaunin birnin Tera ya tabbatar da adadin wadanda suka mutu, inda ya ce harin ya kuma rutsa da mata da kananan yara. Ya kara da cewa wasu da dama sun jikkata kuma an garzaya da su asibiti.

Yankin Tillaberi, wanda ke makwabtaka da Mali da Burkina Faso, ya zama daya daga cikin wuraren da kungiyoyin ‘yanta'adda masu alaka da Daesh suka fi kai hare-hare.

Tillaberi na cikin yankunan da suka fi fama da asarar rayukan fararen-hula

A cewar kungiyar ACLED mai sanya ido kan rikice-rikice, yankin Tillaberi ne ya fi kowanne yankin tsakiyar Sahel yawan mace-macen fararen-hula a bara, inda fararen-hula suka fi fuskantar hare-hare.

Kungiyar ta danganta karuwar tashin hankalin da ke yankin da muhimmancin wurin da yankin yake, kasancewar yana kan iyakar kasashen Nijar, Burkina Faso da Mali, inda kungiyoyin ‘yanta'adda ke gudanar da ayyukansu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan rabin mutane 450,000 da aka yi wa rajistar zama ‘yan gudun hijira a cikin gida a Nijar a bara suna zaune ne a yankin Tillaberi.