| Hausa
WASANNI
4 minti karatu
Nijar ta tabbatar wa CAF shirinta na neman karɓar baƙuncin AFCON 2032 tare da Mali da Burkina Faso
Duk da cewa wakilan hukumar CAF ba su yi magana da manema labarai ba bayan rangadin, masu kula da ƙwallon ƙafa a Nijar na ganin baƙin sun gamsu.
Nijar ta tabbatar wa CAF shirinta na neman karɓar baƙuncin AFCON 2032 tare da Mali da Burkina Faso
Jami'an hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijar, FENIFOOT, sun gabatar da bayanai game da ƙasar shirin ƙasar na kasance cikin masu karɓar baƙuncin AFCON 2032

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijar (FENIFOOT) ta jaddada shirinta na neman karɓar baƙuncin gasar AFCON ta 2032 tare da Mali da Burkina Faso ga wakilan hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF).

Shugaban FENIFOOT, Issaka Adamou, ya bayyana haka ne bayan tawagar CAF ta ziyarci muhimman ababen more rayuwa da ke da alaƙa ga neman karɓar baƙuncin wasan na haɗin gwiwa a babban birnin Nijar, Yamai, ranar Talata.

Tawagar da ta samu shugabancin wani jami’in CAF mai suna Basegeta Avellin ta halarci gabatarwa game da neman karɓar baƙuncin na Nijar da kuma matakan tsaro da aka ba da shawarar ɗaukawa game da gasar AFCON ta 2032 wanda FENIFOOT gabatar tare da ziyartar otel-otel da kuma filayen wasanni.

Kamfanin dillancin labaran Nijar (ANP) ya ba da rahoton cewa filayen wasannin da suka ziyarta sun haɗa da filin wasan tunawa da Janar Seyni Kountché (wanda ake gyarawa) da kuma filayen da ake gefensa, sai kuma filin wasa na cikin gari da kuma Cibiyar Fasaha ta Ƙasa.

Duk da cewa wakilan CAF ba su yi magana da manema labarai bayan rangadinsu ba, jami’an hukumar ƙwallon ƙafar Nijar suna ganin baƙin sun gamsu.

"Ba za ni ari bakinsu na ci albasa ba, amma ina ganin sun gamsu da abin da suka gani da kuma abin da suka ji, musamman bisa daidaito a bayanan," kamar yadda kamfanin ANP ya ambato shugaban FENIFOOT, Issaka Adamou, yana cewa.

Bayan ya bayyana taƙaici game da rashin filayen wasa da aka amince a yi wasa cikinsu a ƙasar a halin yanzu, don yadda filin wasan tunawa da Janar Seyni Kountché yake a lalace, shugaban hukumar FENIFOOT ya tabbatar da cewa za a gyara shi a cikin watanni masu zuwa a wani ɓangare na neman karɓar baƙuncin gasar AFCON ɗin, kamar yadda ANP ya ruwaito.

"Saboda wannan, muna ganin a shekarar 2027, za a samu wannan cikakken gyaran kuma cikakken gyara filin wasan tunawa da Janar Seyni Kountchéé ne," kamar yadda ANP ya ambato shi yana cewa.

 "A cikin bayanin aikinmu, mun bayyana cewa a cikin shekarar 2028 zuwa 2029, za a gina wani filin wasa na biyu, wanda mun riga mun ba shi suna Filin wasan Sake Kafa ƙasa."

Takardar neman karɓar baƙuncin gasar na Nijar da ANP ya samu ta nuna cewa filin wasan tunawa da Janar Seyni Kountché (wanda ake gyarawa) zai iya ɗaukar kujeru 30,000 kuma kasafin kuɗin gyara shi dalar Amurka miliyan 26.09 ko abin da ya ɗara CFA biliyan 15 ne, yayin da filin wasan Sake Kafa Ƙasa, wanda gina shi yana mataki na shiri, zai kasance yana da kujeru 20,000 da kasafin kuɗin da ya ɗara kuɗin CFA biliyan 25.

Baya ga waɗannan akwai ginawa ko kuma gyara filayen atisaye takwas da kasafin kuɗi da ya kai dala miliyan $21.20 ko kuma abin da ya ɗara CFA biliyan 12.

Da yake magana game da otel-otel, Issaka Adamou ya ce ba shi da damuwa game da su.

"A wannan matakin, ba mu damu ba sosai," in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa a Yamai, "muna da isassun otel-otel, musamman tunda dai akwai Gawai hotel wanda ake gyarawa saboda ɗaya ne daga cikin muhimman ote-otel a cikin takardar neman karɓar baƙuncinmu, saboda wani otel ne da za mu iya saka tawaga 3 zuwa 4 a cikinsa," kamar yadda ya bayyana.

Takardar neman karɓar baƙuncin gasar ta kuma bayyana jumullar ote-otel 18 a Yamai, inda adadin ɗakunansu ya kai 1,620, in ji ANP.

Da yake bayanin kan abin da ya sa aka zaɓi Yamai a matsayin inda za a gina filin wasan na biyu maimakon wasu birane a can cikin ƙasar, Issaka ya bayyana cewa "Sharruɗan ba kawai game da filin wasan ƙwallon ƙafa ba ne kawai. Idan ka gina filin wasa a wani wuri, za ka buƙaci aƙalla otel-otel masu darajar tauraro 4 domin kasancewa masauƙi ga tawagogin da ke cikin rukunin da za su yi wasa a wannan filin wasan. Wannan wani abu ne da ba mu da su a can cikin ƙasar." 

"Wannan shi ya sa muka zaɓi gina filayen wasan biyu a cikin Yamai. Saboda a Yamai, mun riga mun muna da wuraren masauƙin baƙi da za su iya aikin, kamar yadda ake cewa," in ji shi.

Shugaban na FENIFOOT ya kuma yi magana game da kayayyakin jinya na birnin, yana mai cewa su ma kansu ‘yan Nijar sun yi mamakin ganin cewa asibitin ƙwararru na Yamai yana da ƙwarewa fiye da yadda suke tsammani, yana mai ƙarawa da cewa yana ganin babu wani abin damuwa game da jinya.