| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Ƙungiyoyin ƙwadago da na ɗalibai na shirin gudanar da sabuwar zanga-zanga a Faransa
Zanga-zangar na zuwa ne bayan makonni da dama da matasa suka shafe suna tayar da tarzoma da kuma yajin aikin gama-gari a faɗin ƙasar, waɗanda suka jawo dubban ɗaruruwan ma'aikata fita kan tituna.
Ƙungiyoyin ƙwadago da na ɗalibai na shirin gudanar da sabuwar zanga-zanga a Faransa
Ministan Harkokin Cikin Gida na Faransa, Laurent Nunez, ya ce za a jibge jami'an 'yansanda da sauran jami'an tsaro 70,000 a sassan ƙasar domin tabbata

Ƙungiyoyin ƙwadago da na ɗalibai a Faransa na shirin sake gudanar da zanga-zanga a ranar Asabar, yayin da masu fafutukar ƙungiyar Yellow Vests su ma ke shirin gudanar da wata zanga-zanga ta daban a tsakiyar birnin Paris, duk da haramcin da hukumomi suka sanya.

Zanga-zangar na zuwa ne bayan makonni da dama da matasa suka shafe suna tayar da tarzoma da kuma yajin aikin gama-gari a faɗin ƙasar, waɗanda suka jawo dubban ɗaruruwan ma'aikata fita kan tituna.

Hakan na faruwa ne ƙasa da watanni shida kafin 'yan ƙasar su zaɓi wanda zai gaji Shugaba Emmanuel Macron, a daidai lokacin da jam'iyyun masu tsattsauran ra'ayi ke kan gaba a sakamakon kuri'un jin ra'ayin jama'a.

Ƙungiyoyin ɗalibai da na ƙwadago sun shirya gudanar da wani tattaki da hukumomi suka amince da shi a tsakiyar birnin Paris, ƙarƙashin taken “Yaƙi da tsadar rayuwa da kuma nuna goyon baya ga matasa.”

Sai dai masu fafutukar ƙungiyar Yellow Vests sun ƙi shiga tattakin, inda a maimakon haka suka kira magoya bayansu zuwa wata zanga-zanga a dandalin Place de la Concorde, kusa da majalisar dokokin ƙasar da fadar shugaban ƙasa, wuraren da hukumomi suka haramta gudanar da zanga-zanga.

Ministan Harkokin Cikin Gida na Faransa, Laurent Nunez, ya ce za a jibge jami'an 'yansanda da sauran jami'an tsaro 70,000 a sassan ƙasar domin tabbatar da tsaro.

Ya ce: “Idan aka samu masu tayar da tarzoma ko masu wawushe dukiyoyi, za mu kasance a shirye domin tunkararsu.”

Yawancin zanga-zangar da aka gudanar sun kasance cikin lumana, duk da cewa wasu sun rikide zuwa rikici da lalata kadarori, ciki har da zanga-zangar ranar 17 ga Oktoba, wadda ta haifar da mafi munin tarzoma da Faransa ta gani cikin shekaru da dama.

A ranar Alhamis, dubban daruruwan ma'aikatan da ke yajin aiki sun gudanar da tattaki a sassan ƙasar, inda mafi yawancin zanga-zangar suka gudanar da ita cikin lumana, duk da cewa an samu arangama a wasu birane.