| Hausa
TATTALIN ARZIKI
2 minti karatu
Nijeriya ta amince da a haƙo sabbin rijiyoyin mai 145 a shekarar 2026
Mahukunta sun ce Nijeriya na da injinan haƙar mai fiye da 100, inda a bana 46 daga cikinsu ke aiki, adadin da ya karu da fiye da kashi 300 idan aka kwatanta da na shekarar 2021.
Nijeriya ta amince da a haƙo sabbin rijiyoyin mai 145 a shekarar 2026
Hukumar NUPRC ta ce tana ci gaba da ɗaukar matakan dakile satar ɗanyen mai a sassan daban-daban na ƙasar.

Hukumar kula da harkokin haƙo mai ta Nijeriya ta amince da sabbin ayyukan haƙo rijiyoyin mai 145, da sake buɗe tsofaffin rijiyoyi 595 da kuma tsare-tsaren raya filayen mai (FDPs) guda 39 a wannan shekara ta 2026.

Hakan na daga cikin ƙoƙarin da ƙasar ke yi na ƙara yawan man da take hakowa, tare jawo hankalin masu zuba jari da kuma ƙarfafa tsaron makamashi, kamar yadda wani babban jami'in hukumar ya bayyana a ranar Talata.

Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Nijeriya (NUPRC) ta ce matakin amincewar da aka dauka na nuna yadda ake saurin tantance ayyukan kamfanonin mai, lamarin da ya taimaka wajen rage jinkiri da kuma kuɗin gudanar da ayyukan.

“Ya zuwa yanzu a wannan shekarar, mun amince da tsare-tsaren raya filayen mai guda 39, sabbin ayyukan haƙo rijiyoyi 145 da kuma sake buɗe tsofaffin rijiyoyi 595,” a cewar shugabar hukumar, Oritsemeyiwa Eyesan.

Ta bayyana hakan ne a wani taron masana'antar mai da aka gudanar a jihar Legas.

Eyesan, wadda mataimakin daraktan kula da tafkunan mai na hukumar, Ahmad Abdullahi, ya wakilta, ta ce saurin amincewa da ayyukan na taimaka wa kamfanonin mai wajen aiwatar da shirye-shiryen da za su ba su damar cim ma burinsu na haɓaka samar da mai da kuma inganta samar da makamashi.

Ta ƙara da cewa Nijeriya na da injinan haƙar mai fiye da 100, inda a bana 46 daga cikinsu ke aiki. Adadin ya nuna ƙarin fiye da kashi 300 idan aka kwatanta da irin wannan matakin da aka samu a shekarar 2021.

Eyesan ta kuma bayyana cewa kamfanonin da ke gudanar da binciken yanayin ƙasa ta hanyar amfani da na'urorin girgizar ƙasa (seismic companies) sun zuba jarin fiye da dala miliyan 100 a Nijeriya tun bayan fara aiki da dokar masana'antar man fetur ta ƙasar wato (Petroleum Industry Act) shekaru uku da suka wuce.

Ta ce jarin ya taimaka wajen inganta bayanan binciken ƙasa da kuma ƙarfafa ƙoƙarin gano sabbin ma'adinan mai da iskar gas.

Haka kuma hukumar NUPRC ta ce tana ci gaba da ɗaukar matakan dakile satar ɗanyen mai a sassan daban-daban na ƙasar.