| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Greenpeace ta gargaɗi Ghana kan barazanar shara sakamakon shigo da tsofaffin tufafi miliyan 1 a mako
Wani bincike ya nuna cewa yawan tsofaffin tufafin da ake shigo da su Ghana na wuce buƙatar al'ummar ƙasar, lamarin da ke barazana ga tsarin kula da shara.
Greenpeace ta gargaɗi Ghana kan barazanar shara sakamakon shigo da tsofaffin tufafi miliyan 1 a mako
Gurɓatar muhalli na kuma barazana ga tafkin Korle Lagoon, wanda ke tara ruwan da ke kwararowa daga sassa daban-daban na Accra.

Wani katafaren wurin zubar da shara a birnin Accra, babban birnin Ghana, na ƙara zama barazana ga lafiyar al'umma da muhalli, inda dubban mazauna yankin da masu tattara shara ke fuskantar haɗari.

Ƙungiyoyin kare muhalli sun yi gargaɗin cewa ƙasashen Yamma sun mayar da Ghana wata babbar matattarar tsofaffin tufafi da na'urorin lantarki da ba sa buƙata.

Ƙungiyar Greenpeace ta kiyasta cewa ana jigilar kusan tsofaffin tufafi miliyan 15 zuwa Ghana a kowane mako, inda kusan rabinsu ke zama shara bayan ’yan kasuwa sun ware waɗanda za a iya sayarwa.

“A zahiri, ƙasashen Arewa na amfani da Ghana a matsayin wajen zubar da sharar da masana'antar tufafi ke samarwa,” in ji Samuel Quansi-Idun, shugaban sashen bincike na Greenpeace Afrika, a wata hira da kamfanin dillancin labarai na AFP.

Wani bincike da Greenpeace ta gudanar ya nuna cewa Ghana ta shigo da tsofaffin tufafi sama da tan 110,000 a shekarar 2022. Ƙungiyar ta ce yawan tufafin ya zarce buƙatar cikin gida, lamarin da ke ƙara wa tsarin kula da shara na ƙasar nauyi.

Illolin tsofaffin tufafi da na'urorin lantarki ga lafiya

Masana lafiyar muhalli sun yi gargaɗin cewa ƙona tsofaffin na'urorin lantarki da wayoyinsu na iya sakin sinadarai masu guba, kamar gubar dalma da sinadarin mercury. Haka kuma, hayaƙin da ke tashi daga irin waɗannan gobara na ɗauke da baƙin hayaƙi da wasu sinadarai masu illa ga lafiya.

Greenpeace ta kuma gano cewa kashi 89 cikin 100 na tsofaffin tufafin da ta bincika sun ƙunshi zaren roba da ake ƙerawa daga sinadaran man fetur, kamar polyester.

Irin waɗannan zare na iya sakin ƙananan ƙwayoyin robobi yayin da suke lalacewa, tare da sakin sinadarai masu haɗari idan aka ƙone su.

“Wannan ba matsalar muhalli kaɗai ba ce, matsala ce da ke barazana ga lafiyar ɗan Adam,” in ji Hellen Kahaso Dena, masaniyar yaƙi da gurɓatar muhalli ta robobi a Greenpeace.

Gurɓatar muhalli na kuma barazana ga tafkin Korle Lagoon, wanda ke karɓar ruwan da ke kwarara daga sassa daban-daban na Accra.

Masana kimiyya sun yi gargaɗin cewa gurɓatattun sinadarai daga wuraren zubar da shara na iya kutsawa cikin ƙasa da hanyoyin ruwa, daga bisani su shiga cikin abincin da al'umma ke ci.

Ghana na ƙoƙarin shawo kan matsalar shara

Wannan gargaɗi na zuwa ne a daidai lokacin da batun kula da shara ke ƙara samun muhimmanci a tattaunawar sauyin yanayi ta COP31 da ake gudanarwa a Turkiyya.

A watan Satumba, Shugaban Ghana, John Mahama, ya ƙaddamar da aikin tsaftace muhalli na tsawon watanni uku, da nufin kwashe kusan tan miliyan ɗaya na shara daga babban birnin ƙasar.

Ministan Ƙananan Hukumomi, Mahama Ayariga, ya ce gwamnati za ta shigar da masu tattara shara ba bisa ƙa'ida ba cikin tsarin sake sarrafa shara na hukuma.

Ya ƙara da cewa gwamnati na fatan samar da guraben ayyukan yi na dindindin har guda 20,000 a fannonin kula da shara da tattalin arzikin sake amfani da albarkatu (circular economy).