| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Jihar Katsina ta kaddamar da jami'an kula da gandun daji fiye da 1,000 domin magance matsalar tsaro
Gwamnan ya tabbatar wa jami’an cewa gwamnatinsa za ta samar musu da kayan aiki da sauran tallafin da suke buƙata domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Jihar Katsina ta kaddamar da jami'an kula da gandun daji fiye da 1,000 domin magance matsalar tsaro
Gwamna Radda ya buƙace su da su gudanar da aikinsu bisa gaskiya da ƙwazo, tare da zama jakadu na gari ga ƙasarsu da kuma al’ummomin da suke wakilta. / Facebook/DikkoRadda

Gwamnatin jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Nijeriya ta ƙaddamar da jami’an kula da gandun daji 1,008 a wani mataki na ƙarfafa tsaro a dazuzzuka da kuma yaƙi da ayyukan ’yan bindiga, ’yan ta’adda, masu satar shanu da masu sare bishiyoyi ba bisa ƙa'ida ba.

Gwamnan jihar, Dikko Radda, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin bikin yaye jami’an da aka horas a birnin Katsina.

Ya buƙace su da su gudanar da aikinsu bisa gaskiya da ƙwazo, tare da zama jakadu na gari ga ƙasarsu da kuma al’ummomin da suke wakilta.

Radda ya ce jami’an za su yi aiki tare da kusan mambobi 3,000 na rundunar tsaron sa-kai ta Community Watch Corps ta jihar, da rundunar Civilian Joint Task Force, da ’yan sintiri da mafarauta domin tabbatar da tsaro a dazuzzuka da sauran wuraren da ke fuskantar barazanar tsaro a faɗin jihar.

Gwamnan ya tabbatar wa jami’an cewa gwamnatinsa za ta samar musu da kayan aiki da sauran tallafin da suke buƙata domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ya koka kan yadda dazuzzukan jihar, waɗanda a baya suke zama hanyar samun abin dogaro ga al’ummomin da ke kewaye da su, suka koma mafakar masu aikata laifuka.

Sai dai Radda ya bayyana matakan da gwamnatinsa ta ɗauka, ciki har da kafa rundunar Community Watch Corps da kuma tallafa wa hukumomin tsaro na yau da kullum, yana mai cewa sun taimakawa matuƙa wajen rage ayyukan ’yanbindiga da ta’addanci a jihar.

Gwamnan ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu bisa ƙaddamar da shirin kafa jami’an tsaron dazuzzuka a jihohi da dama, yana mai bayyana matakin a matsayin wani muhimmin ƙoƙari na tabbatar da tsaro a dazuzzukan Najeriya.

A baya, mai horas da jami’an tsaron dazuzzukan, Laftanar Kanal George Agar, ya bayyana cewa jami’an 1,008 da suka kammala horon sun haɗa da maza 990 da mata 18, waɗanda suka shafe makonni takwas suna samun horo mai ƙarfi.

Ya ce horon ya ƙunshi dabarun tunkarar yanayi daban-daban na yaƙi, ciki har da sarrafa bindigogin AK-47, tattara bayanan sirri, gudanar da samame da dare, tunkarar waɗanda ake zargi da ta’addanci, ceto mutanen da aka sace da kuma hana sare bishiyoyi ba bisa ƙa’ida ba.