Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya gudanar da jerin ganawa ta kai-tsaye da shugabannin ƙasashe da dama a gefen taron COP31 da ke gudana a birnin Antalya.
Daga cikin waɗanda ya gana da su akwai shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, da Firaministan Bangladesh Tarique Rahman, da Firaministan Habasha Abiy Ahmed Ali, da Ministan Makamashi na Saudiyya Yarima Abdulaziz bin Salman Al Saud, da shugaban kuma Majalisar al’ummar Turkmenistan Gurbanguly Berdimuhamedov.
Turkiyya ce a bana take karɓar bakuncin taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi a birnin Antalya da ke kudancin ƙasar, daga ranar 9 zuwa 20 ga watan Nuwamba.
Sannan Ma’aikatar Muhalli, Birane da Sauyin Yanayi ta Turkiyya ta ce ana sa ran shugabanni 102 waɗanda ke wakiltar ƙasashe 95 da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa bakwai ne za su halarci taron.
Taron ya haɗa dukka ƙasashe 196 da ke cikin yarjejeniyar sauyin yanayi da kuma Tarayyar Turai, inda daga cikin mahalarta taron akwai shugabannin ƙasashe 37 da kuma firaministoci 35.
Brazil: Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva
Shugaban Brazil, Lula, wanda ya isa Antalya domin halartar taron COP31, ya tattauna da Erdogan a ranar Talata kan dangantakar ƙasashen biyu da kuma batutuwan da suka shafi yankuna da duniya, a cewar Hukumar Yaɗa Labaran Fadar Shugaban Ƙasar Turkiyya.
Erdogan ya ce ƙasashen biyu za su cika shekaru 100 da kulla hulɗar diflomasiyya a shekarar 2027, yana mai cewa za su ci gaba da faɗaɗa haɗin gwiwarsu, musamman a fannonin kasuwanci da masana'antar tsaro.
Ya ƙara da cewa ƙasashen biyu suna ba da muhimmanci ga zaman lafiya wajen tunkarar matsalolin ƙasa da ƙasa, tare da jaddada muhimmancin haɗin kai da goyon bayan juna.
Bangladesh: Firaminista Tarique Rahman
Tattaunawar Erdogan da Firaministan Tarique Rahaman ta mayar da hankali kan dangantakar Turkiyya da Bangladesh da kuma batutuwan yankin, kamar yadda hukumar ta bayyana.
Shugaban na Turkiyya ya ce ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu, musamman a fannonin kasuwanci da masana'antar tsaro, zai amfani ɓangarorin biyu.
Ya kuma ce Ankara na ci gaba da jawo hankalin ƙasashen duniya kan halin jinƙai da ake ciki a Cox’s Bazar, inda kimanin 'yan Rohingya miliyan ɗaya ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira.
Habasha: Firaminista Abiy Ahmed Ali
Erdogan da Firaminista Abiy Ahmed sun tattauna kan dangantakar ƙasashensu da kuma batutuwan yankin, kana shugaban na Turkiyya ya yi alƙawarin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni daban-daban, musamman kasuwanci da zuba jari.
Kazalika ya jaddada goyon bayan Ankara ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Habasha.
Haka kuma, Erdogan ya taya Abiy murnar shirye-shiryen da Habasha ke yi na karɓar bakuncin taron COP32 a shekara mai zuwa, bayan da Turkiyya ta jagoranci taron na bana.
Saudiyya: Ministan Makamashi Yarima Abdulaziz bin Salman Al Saud
Erdogan ya kuma gana Ministan Makamashi na Saudiyya, Yarima Abdulaziz bin Salman Al Saud, a gefen taron.
A yayin ganawar, Ministan Makamashi da Albarkatun Ƙasa na Turkiyya, Alparslan Bayraktar, ya sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakanin ƙasashen biyu.
Shugaban COP31 kuma Ministan Muhalli na Turkiyya, Murat Kurum, da Ministan Harkokin Waje na kasar Hakan Fidan, da Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Hasan Dogan da Daraktan Yaɗa Labarai Burhanettin Duran sun halarci ganawar.
Turkmenistan: Shugaban Majalisar al’ummar Gurbanguly Berdimuhamedov
Haka kuma Erdogan ya gana da Gurbanguly Berdimuhamedov, wanda shi ne jagoran al'ummar Turkmenistan kuma shugaban Majalisar Jama'ar ƙasar, a cewar fadar shugaban Turkiyya.
Shugabannin biyu sun tattauna kan dangantakar ƙasashensu da kuma batutuwan da suka shafi yankunansu da duniya baki ɗaya.
Sun jaddada muhimmancin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannonin makamashi, kasuwanci, tsaro da kuma zuba jari.
A halin da ake ciki, wasu shugabannin ƙasashe na ci gaba da isa birnin Antalya domin halartar taron COP31. Shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev shi ne shugaba na baya-baya da ya isa birnin a ranar Talata bisa gayyatar Erdogan, kamar yadda fadar shugaban ƙasar Azerbaijan ta bayyana.
Erdogan, wanda ya riga ya gana da Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres da sauran shugabannin da aka ambata, ana sa ran zai ci gaba da gudanar da ƙarin tattaunawa yayin da babban taron ke ci gaba da gudana.




























