| Hausa
TURKIYYA
4 minti karatu
Erdogan na Turkiyya: 'Babu wata damar rarrabuwar kai a duniyar Turkawa'
Shugaban Turkiyya Erdogan ya ce taron na Ankara zai ƙarfafa hadin kai,inda Turkiyya ta shirya domin kasancewa shugabar Ƙungiyar Ƙasashen Turkawa.
Erdogan na Turkiyya: 'Babu wata damar rarrabuwar kai a duniyar Turkawa'
Erdogan yana jawabi a wata liyafar da aka shirya wa shuwagabannin Ƙungiyar Ƙasashen Turkawa Ankara, wwanda ke karɓar baƙuncin taron OTS na 13.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana haɗin a tsakanin ƙasashen Turkawa a matsayin wata “buƙata ta dabara” a cikin tashe-tashen hankula na duniya, gabanin taro na 13 Ƙungiyar Ƙasashen Turkawa (OTS) a Ankara.

“Siyasar Duniya na sauyawa sosai. A wani lokacin da tsarin duniya ke fama da ƙoƙarin samar da adalci da amana kuma yaƙe-yaƙe da tashe-tashen hankula suna shafar yankuna masu yawa, haɗin kai tsakanin ƙasashen Turkawa ya zama buƙatar dabara mai muhimmanci,” kamar yadda Erdogan ya bayyana a wata maƙala da aka wallafa a kafafan watsa labarai a faɗin ƙasashe mambobin ƙungiyar da kuma ƙasashe masu sa ido.

Ya ce haɗin kan ƙasashen Turkawa shi ne “bayani mafi ƙarfi” na tarihinsu da kuma jajircewarsu na tsara makomarsu ta bai ɗaya.

Da yake jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin ƙasashen Turkawa, Erdogan ya ce “babu damar rarrabuwar kai ko kuma rashin jituwa a duniyar Turkawa.”

Taron, wanda za a yi a ƙarƙashin jigo mai taken “Ƙarnin Turkawa: Haɗin kai a harshe da tunani da aiki,” zai ƙara ƙarfafa wannan jajircewar, a cewar Erdogan.

Turkiyya za ta karɓi shugabancin ƙungiyar daga Azerbaijan, wani mataki da Erdogan ya bayyana a matsayin wani mataki mai cike da nauyi mai tarihi na inganta muraɗunsu da kuma ƙarfafa ikon hukuma na OTS.

Haɗin kan tattalin arziki da na tsaro

Haɗin kan tattalin arziki na ɗaya daga cikin muhimman ababen da ƙungiyar ta fi mayar da hankali a kai, kamar yadda Erdogan ya bayyana, yana mai nuna hanyar yankin Caspian zuwa gabashi da yammacin yankin a matsayin muhimmiyar dama ta faɗaɗa alaƙar cinikayya da sufuri tsakanin Asia da Turai.

“Yankin Turkawa na da yiwuwar zama ɗaya daga cikin muhimman cibiyoyi na sufuri da jigilar kayayyaki na duniya,” in ji shi.

Ya yi kira da a samu ƙarin alaƙa na layin dogo da tashoshin jiraen ruwa da hanya da kwstom tare da amfani yadda ya dace da asusun zuba jari na ƙasasashen Turkawa da ma’adinai na makamashi da kuma iko na makamshiun da ake iya sabuntawa.

Ya kuma yi kira ga ƙasashe mambobin ƙungiyar su ƙarfafa ƙere-ƙre da zuba jari da da fasaha a sadarwa.

Erdogan ya ce ya kamata haɗin kai zarce zuwa harkar tsaro inda ƙasashe mambobi za su haɗa ƙrfi da ƙrfe domin magance ta’addanci da aikata laifi mai ƙta kan iyakoki da barazana na intanet.

Ya bayyana haɗin kai a masana’antar tsaro, ciki har da musayar ƙarewa da samar da fasahohi na cikin gida da kuma faɗaɗa ayyuka na hadin gwiwa.

Tarihi na bai ɗaya

Erdogan ya bayyana tarin al’adu a matsayin ginshiƙin haɗin kai, yana mai ishara ga fitattun mutane irin su Khoja Ahmed Yasawi da Ali Shir Nava'i da Nizami Ganjavi da Magtymguly Pyragy da Yunus Emre da kuma Chinghiz Aitmatov.

Ya ce haɗin kai kan harrufa Turkanci na bai ɗaya wani mataki ne mai cike da tarihi wajen kai ga hadin kai na al’ada kuma ya yi kira ƙrin haɗin kai a fannin ilimi da kimiyya da fasahar wallafa littatafai da ta dijital.

Batutuwa na yanki da kuma ‘yancin Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus

A kan batun yankin South Caucasus, Erdogan ya ce yankin South Caucasus mai zaman lafiya da kwanciyar hankali zai ba da "muhimman damarmaki " ga ƙasashe na yankin da kuma ɗaukacin duniyar Turkawa gabaɗaya.

Ya yi kira ga ƙasashen Turkawasu "ƙara matsa kaimi" wajen cim ma mafita mai adalci ga batun Falasɗinu, yana mai kira da gudmowa ta samar da tallafi na jinƙai ga Gaza da kuma ƙddamar da ƙoƙarin sake ginawa da zaran damar yin hakan ta samu.

Shugaban Turkiyyan ya kuma sake tabbatar da goyon baya ga Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus, yana mai cewa Türkiyya za ta ci gaba da kare ;yancinsu da muradunsu da kuma neman kawo ƙarshen wariyar da ake musu mara adalci.

Ya yi kira da a faɗaɗa damarmaki da matsayar mai sa ido da Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus take da ita a ƙungiyar OTS da kuma ƙarfafa alaƙrta da sauran jamhuriyoyin Turkawa.

Ya kuma bayyana cewa Turkiyya na fatan cewa za a magance sabunta tashin hankalin Iran ta hanyar diflomasiyya maimakon ta makamai.

Erdogan ya ce ƙungiyar za ta iya ba da gudumowa ga zaman lafiyar yanki da na duniya ta hanyar mayar da ƙudurin siyasa nasarori masu ɗorewa.

“Na yi manin cewa ƙarni na 21 zai kasnace ‘Ƙarni na Duniyar Turkawa’,” in ji shi, yana mia ƙrawa da cewa taron na Ankara zai buɗe sabbin hanyoyi na haɗin kai da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashe mambobin ƙungiyar.