| Hausa
TURKIYYA
3 minti karatu
'Turkiyyar yau ta fi ta bara karfi,' in ji Shugaba Erdogan a Ranar Jamhuriya
Shugaban ƙasar Turkiyya ya yi bikin cikar ƙasar shekaru 103 da zama Jamhuriya, inda ya nuna ƙarfin da Turkiyya za ta ci ƙara samu a nan gaba ta hanyar samun ci-gaba a fannin tsaro da diflomasiyya.
'Turkiyyar yau ta fi ta bara karfi,' in ji Shugaba Erdogan a Ranar Jamhuriya
(TSOHON HOTO) Erdogan ya ce jajircewa da ƙarfin halin da aka nuna a shekaru 103 da suka wuce sun ci gaba da ƙarfafa Turkiyya a yau. / Anadolu Agency

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ranar Alhamis ya ce ƙasarsa tana tabbatar da zaman lafiya a yayin da take ɗaukar nauyin magance rikice-rikice da yaƙe-yaƙe a maƙotanta da wasu sassan duniya.

A wani saƙon bidiyo domin bikin cikar ƙasar shekaru 103 da zama Jamhuriya, Erdogan ya taya murna ga ƙasar Turkiyya da Turkawa mazauna Arewacin Cyprus da sauran ‘yan ƙasar da ke zanue a ƙasashen duniya bisa zagayowar ranar 29 ga watan Oktoba.

Kazalika ya miƙa gaisuwa ga baƙi da ke ofisoshin jakadancin Turkiyya da kuma al’ummomin duniya da ke zaune a yankin Turkiyya bisa taya ƙasar murna.

Erdogan ya ce jamhuriya ita ce manufa mafi girma da ke nuna jajircewar Turkiyya ta zama ba tare da kyara ba da kuma cin gashinta da kyautata makomarta.

Ya ce fafutukar da ƙasar ta yi wadda Mustafa Kemal Ataturk, mutumin da ya kafa Jamhuriyar Turkiyya ya jagoranta, ta nuna irin tagomashin da haɗin kan ƙasa ke iya samarwa har a lokacin da ake fama da tsanani.

Fafutukar ƙasa da ‘yancin kai

Nasarar da aka samu, duk da ƙalubalen da aka fuskanta, ta sauya makomar ƙasar da ‘yancinta na zama mai cin gashin kanta, in ji shi.

Erdogan ya ce Turkiyya za ta ci gaba da wanzar da zaman lafiya da adalci bisa taken “Zaman lafiya a cikin gida da zaman lafiya a duniya”.

Ya ce jajircewar da ƙasar ta nuna shekaru 103 da suka wuce ta ci gaba da ƙarfafa gwiwar ƙasar, inda ta nuna wannan ci-gaba a cikin shekaru 24 a fannin tsaro da makamashi da sufuri da diflomasiyya abubuwan da suka sa Turkiyya ta zama ƙasa mai ƙarin ƙarfi da yalwa.

Shugaban ƙasar ya ce ƙasarsa tana samar da fasahohi nata na kanta da faɗaɗa harkokin tsaro da tsaron makamashi da sabunta kayayyakin sufuri da ƙara ƙarfin ƙere-ƙere.

Manufar Turkiyya a nan gaba

Erdogan ya ce ƙasarsu mai mutum miliyan 86 za ta tabbatar da shirinta na “Turkiyya ta Ƙarni” zuwa wani babban ci-gaba da kuma jagorantar ƙasar domin samun ci-gaba mai ɗorewa.

“Mun gode wa Allah, Turkiyya tana da ƙarfi a yau fiye da yadda take a baya. Da yardar Allah, gaba za ta fi baya kyau, sannan za ta fi samun girmamawa da tasiri a ko wane fanni,” in ji shi, inda ya ƙara da cewa ƙasar Turkiyya za ta tabbatar da tasirinta a wannan ƙarni.

Ya kammala da tunawa da Ataturk da abokan gwagwarmayarsa da sauran gwaraza da suka yi fafutuka da ma waɗanda suka rasa rayukansu domin kare martabar ƙasar, inda ya jinjina musu.

“Muna murnar cika shekara 103 da samun jamhuriyarmu,” in ji shi.