| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Antalya ya karɓi masu yawon buɗe ido miliyan 14 daga ƙasashen waje duk da ƙalubalen duniya
Wani wakilin fannin yawon buɗe ido ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
Antalya ya karɓi masu yawon buɗe ido miliyan 14 daga ƙasashen waje duk da ƙalubalen duniya
Mazauna da masu yawon buɗe ido sun taru bakin tekun Konyaalti domin guje wa zafi Antalya, a Turkiyya a ranr 2 ga watan Agustan 2026.

Birnin Antalya na Turkiyya ya karɓi kusan masu yawon buɗe ido miliyan 14 daga ƙasashen waje tun farkon shekarar 2026, lamarin da ke nuna yadda fannin yawon buɗe ido na birnin ke jure ƙalubalen duniya, ciki har da rikicin Gabas ta Tsakiya, yaƙin Rasha da Ukraine da matsalolin tattalin arzikin duniya.

Wani wakilin fannin yawon buɗe ido ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Kaan Kasif Kavaloglu, shugaban Ƙungiyar Masu Otel-otel ta Yankin Bahar Rum (AKTOB), ya ce kakar yawon buɗe ido ta bana ta samu nasara duk da raguwar masu yawon buɗe ido daga ƙasashen waje da kashi 5 cikin 100, sakamakon rikice-rikicen siyasa da tsaro a yankin da kuma durƙushewar tattalin arziki a wasu sassan Turai.

Kavaloglu ya ce fannin yawon buɗe ido na Antalya ya nuna juriya duk da yaƙin da aka shafe kusan shekaru biyar ana yi tsakanin Rasha da Ukraine, waɗanda ke daga cikin muhimman kasuwannin masu yawon buɗe ido na birnin.

Ya ƙara da cewa an samu gagarumin ƙaruwa a yawan baƙi daga Ukraine, Uzbekistan da Hungary a bana, lamarin da ya taimaka wajen rage tasirin raguwar baƙi daga wasu kasuwanni.

Ya ce hutun kaka na Herbstferien a Jamus ya riga ya fara, yayin da masu yawon buɗe ido daga Birtaniya da Rasha ke shirin yin hutu a wannan lokaci. A cewarsa, farashin yawon buɗe ido a watan Oktoba ya fi sauƙi idan aka kwatanta da Yuli da Agusta, lokacin da ake samun yawan masu yawon buɗe ido a lokacin zafi.

Kavaloglu ya kuma bayyana cewa Antalya za ta karɓi baƙuncin taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi, COP31, a watan Nuwamba, inda aka riga aka fara shirye-shiryen tarbar manyan baƙi.

Rumbun Labarai
COP31: Shugabannin duniya za su dasa itatuwan zaitun a bikin ranar dashen itatuwa ta ƙasa a Turkiyya
Za a fara taron COP31 a Turkiyya yayin da ake kiran ɗaukar matakai masu ƙarfi kan sauyin yanayi
Duran na Turkiyya ya yi gargaɗi game da babakere kan algorizin a duniyar dijital
Turkiyya na shirin karɓar baƙuncin babban taron COP31 kan sauyin yanayi a Antalya
Erdogan ya ce ‘Dole a yi aiki da yarjejeniya’ a Gaza, ya soki ta’addancin kama wuri zaunan Isra'ila
Turkiyya za ta zuba jarin dala miliyan 400 a shirin sararin sama, za ta samar da cibiya a Somalia
Matar Shugaban Turkiyya, Emine Erdogan, ta buɗe cibiyar al'adu ta Yunus Emre a Koriya ta Kudu
Turkiyya da Koriya ta Kudu sun sa hannu kan yarjejeniyar gina tashar makamashin nukiliya
Erdogan na nema cinikayyar dala biliyan 15 da ƙarin muhimmiyar dangantaka a ziyararsa Koriya ta Kudu
Erdogan na Turkiyya: 'Babu wata damar rarrabuwar kai a duniyar Turkawa'
'Turkiyyar yau ta fi ta bara karfi,' in ji Shugaba Erdogan a Ranar Jamhuriya
Turkiyya ta yi bikin cika shekaru 103 da kafa Jamhuriyarta
Kamfanonin Turkiyya na nuna kayayyakinsu a taron baje kolin kayan tsaro a Nijeriya
Turkiyya na shirin zuba jarin dala biliyan 2 a sufurin sama da na sararin samaniya cikin shekaru uku
Kamfanin Fergani na Turkiyya ya tura tauraron ɗan'adam na gwaji na 6 sararin samaniya
Turkiyya, Qatar da Pakistan da Indonesia za su sanya hannu kan yarjejeniyar masana'antar tsaro
Spain na shirin sayen jirgin horar da mayaka na Hurjet kirar Turkiyya guda 15: Shugaban TAI
Turkiyya ta haramta wa shafukan sada zumunta yi wa 'yan ƙasa da shekara 15 rijista
Yarjejeniyar tsaro ta Makka ba ta ba da izinin kai hari kan ƙasashe ba - Turkiyya
Turkiyya ta yi wa Nijeriya ta’aziyya kan hatsarin jirgin soji