Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, kuma ɗantakarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya fito fili ya bayyana matakan da gwamnatinsa take ɗauka domin magance matsalar tsaro, sakamakon ƙaruwar kashe-kashe da gudun hijira a faɗin ƙasar.
Atiku ya bayyana haka ne bayan wani rahoto da gidauniyar ‘‘Foundation for Investigative Journalism’’ ta wallafa, bisa bayanan cibiyar Centre for Democracy and Development (CDD) na watan Oktoba, wanda ya nuna cewa an kashe mutane 638 sakamakon hare-haren rashin tsaro a cikin watan.
Rahoton ya nuna cewa jihohin Arewa Maso Gabashin Nijeriya ne suka fi fama da asarar rayuka, inda aka kashe mutane 409.
Haka kuma, alƙaluman sun nuna cewa adadin waɗanda suka mutu sakamakon taɓarɓarewar al'amuran tsaro a watan Oktoba ya kai 640, idan aka kwatanta da mutane 396 da suka mutu a watan Satumba.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta kuma bayyana cewa kusan mutane 64,000 ne suka tsere daga hare-hare da tashin hankali a Arewacin Nijeriya zuwa maƙociyarta Nijar tun farkon shekarar 2026.
Haka kuma, ɗaruruwan mutane sun tsere zuwa ƙasar Benin domin neman mafaka.
A wata sanarwa da Phrank Shaibu, Daraktan Sadarwa na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na ADC, ya fitar, Atiku ya ce alƙaluman sun nuna mummunan halin da tsaro Nijeriya ta shiga.
Ya ce kashe-kashen ya jefa iyalan da dama cikin ƙunci tare tilasta wa al'ummomi barin gidajensu saboda rashin tsaro, inda ya ƙara da cewa bai kamata 'yan Nijeriya su riƙa tsallaka iyakokin ƙasarsu zuwa ƙasashen waje domin neman tsira ba.
Atiku ya buƙaci gwamnatin Tinubu ta mayar da kare rayukan al'umma da dukiyoyinsu a matsayin babban abin da ta sa a gaba, tare da ƙarfafa ayyukan jami'an tsaro a yankunan da hare-hare suka fi ƙamari da kuma tallafa wa mutanen da suka rasa matsugunansu.
Ya kuma buƙaci Nijeriya ta kara haɗin gwiwa da ƙasashen maƙota da ƙungiyoyin agaji domin taimaka wa mutanen da suka tsere daga matsugunansu.
Kazalika tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce 'yan Nijeriya na buƙatar cikakken bayani kan matakan da gwamnati ke ɗauka domin kawo ƙarshen kashe-kashe da dawo da zaman lafiya.
Ya kuma buƙaci Shugaba Tinubu da ya ɗauki alhakin taɓarɓarewar tsaro, yana mai cewa kare rayukan al'umma shi ne babban nauyin da ke kan kowace gwamnati, kamar yadda sanarwar ta bayyana.




















