Kocin tawagar Amurka, Mauricio Pochettino, ya yi jawabin bankwana da tawagar Amurka, inda ya zubar da hawaye, jim kaɗan bayan an tabbatar da shi a matsayin sabon kocin Manchester United.
Pochettino ya amince da kwantiragin shekara biyu da rabi tare da United, wanda ke nufin zai koma gasar Firimiya, inda ya taɓa riƙe ƙungiyoyin Tottenham, Chelsea, da Southampton.
Kocin ɗan asalin Argentina ne mai shekaru 54, kuma zai karɓi aikin ne daga hannun Michael Carrick, kocin da aka sallama ranar Alhamis.
Da yake jawabi ga manema labarai ranar Juma’a, Pochettino ya bayyana girman alaƙarsa da tawagar Amurka, wadda ya fara horarwa daga Satumban 2024.
Ya ce, ”Yadda aka saba shi ne saɓanin wannan. Wato a sallame ka kana kuka saboda kana so ka ci gaba da zama. A wannan karon, saɓanin haka ce ta faru. Mataki ne mai matuƙar tsauri, amma a lokaci guda ina cikin shauƙi kan matakin.”
Pochettino zai karɓi ragamar Old Trafford ranar 19 ga Nuwamba bayan ya jagoranci Amurka a wasan da za su buga da Haiti ranar Lahadi, 15 ga Nuwamba.
Wasansa na farko da Manchester United zai zo ranar Lahadi, 22 ga Nuwamba tare da Liverpool. Aikin da ke gabansa zai ƙunshi ceto ƙungiyar daga matsayi na 18 a teburin Firimiya.
Zuwa yanzu a tawagar Amurka Poc ya kai ta gasar Kofin Duniya ta shekarar nan, inda aka fitar da su a zagayen ‘yan-16. Ya jagoranci jimillar wasanni 35 inda ya ci 22. Ba daɗewa ya tsawaita zamansa da shekara huɗu har zuwa ƙarshen 2030 kafin United ta nemi shi.






















