Gwarzon ɗanƙwallon ƙafa, Cristiano Ronaldo zai fara siris fim kan ƙwallon ƙafa, inda zai fito a jarumi cikin sauran jaruman fim, duk da cewa har yanzu yana buga ƙwallo a AlNassr ta Saudiyya.
Ronaldo ya sanar a wani saƙon da ya wallafa a Instagram, cewa tuni an fara aikin ɗaukar shirin fim ɗin mai dogon zango, har ya wallafa wasu hotunan inda ake aiki.
A hotunan bayan-fagen an ga wani ɓangare na filin wasa na ƙungiyar Brentford ta Ingila, wanda ke nun da cewa ana ɗaukar fim ɗin ne a filin wasa na gaske a Ingila.
Wannan na zuwa ne yayin da hamshaƙin mai arziƙin ke ci gaba da faɗaɗa kasuwancinsa a wajen harkokin ƙwallo. Ya zaɓi rungumar harkar fim, inda ya haɗa gwiwa da shahararren tauraron fim ɗan Burtaniya, Matthew Vaughn.
Ronaldo zai fito a matsayin jarumi da sunansa na ainihi. Sai kuma Vaughn da suka kafa kamfanin fim na UR Marv Studios, wanda zai zama babban jarumi mai suna Stanley Dalton, ejan ɗin ‘yanƙwallo mai gwagwarmaya a kasuwar ‘yanwasa.
A cikin fim ɗin mai suna “Day 1s”, akwai kuma tsohon tauraron Arsenal ɗan asalin Faransa, Thierry Henry, wanda shi ma zai fito da sunansa.
Akwai kuma wani jarumin, Dave, wani sanannen mawaƙi ɗan Burtaniya, wanda ke da tsatson Nijeriya.
Ronaldo, mai shekaru 41 ɗan asalin Portugal ne amma ya yi ritaya daga bugawa ƙasarsa wasa a farkon watan nan. Kuma ana kallon shigarsa harkar fim a matsayin shirye-shiryen yin ritayarsa daga ƙwallo bakiɗaya.






















