Ƙasar Sudan ta Kudu ta sake ɗage babban zaɓen ƙasar zuwa ranar 11 ga Fabrairun 2027, kamar yadda sabon jadawalin da hukumar zaɓen ƙasar ta fitar ya nuna.
Wannan wani ƙarin jinkiri ne ga zaɓen farko da ƙasar za ta gudanar tun bayan samun ’yancin kai a shekarar 2011. Ba a bayyana dalilin ɗage zaɓen ba.
An shirya gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisar dokoki ne a ranar 22 ga Disamba.
A watan Satumba, kwamitin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da haƙƙin ɗan Adam a Sudan ta Kudu ya bayyana cewa ƙasar ba ta da isassun matakan kariya da kuma yanayin da ake buƙata domin gudanar da sahihin zaɓe cikin lumana.
“Wannan shi ne jadawalin da muka tsara bayan gudanar da cikakkiyar tattaunawa da masu ruwa da tsaki,” in ji Josephine Achiro Fortelo, kwamishiniyar hukumar zaɓen ƙasar kuma kakakinta, a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar Asabar, inda ta tabbatar da sauya ranar zaɓen.
Sudan ta Kudu ta kasance cikin zaman lafiya a hukumance tun bayan cim ma yarjejeniyar zaman lafiya a shekarar 2018, wadda ta kawo ƙarshen yaƙin basasar da ya shafe shekaru biyar ana yi, tare da salwantar da rayukan ɗaruruwan dubban mutane.




















