| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sufeto Janar na ‘Yansandan Nijeriya ya yi gargaɗi kan ɗora wa mutane laifuka bisa ƙabila ko addini
Disu ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabin buɗe taron Tsaro na Shiyyar Arewa Maso Yamma a Gusau inda ya yi kira da a ɗauki matakan yaƙi da rashin tsaro na yankin bisa amfani da bayanan sirri, goyon bayan al’umma.
Sufeto Janar na ‘Yansandan Nijeriya ya yi gargaɗi kan ɗora wa mutane laifuka bisa ƙabila ko addini
Disu ya jaddada muhimmiyar rawar da sarakunan gargajiya da al’ummomin yankuna ke takawa wajen samar da sahihan bayanan sirri

Sufeto Janar na ’Yansandan Nijeriya, Olatunji Disu, ya yi gargaɗi game da ɗora wa mutane laifuka bisa la’akari da ƙabila ko addininsu, yana mai jaddada cewa aikata laifi ba shi da alaƙa da ƙabila, sannan ta’addanci ba shi da addini.

Disu ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabin buɗe taron Tsaro na Shiyyar Arewa Maso Yamma (North-West Security Summit) a Gusau da ke Jihar Zamfara a ranar Laraba, inda ya yi kira da a ɗauki matakan yaƙi da rashin tsaro na yankin bisa amfani da bayanan sirri da neman goyon bayan al’umma da kuma haɗin gwiwa tsakanin jihohi.

Ya buƙaci masu ruwa da tsaki su mayar da hankali wajen ganowa da tantancewa da kuma gurfanar da ƙungiyoyin masu aikata laifuka a gaban kotu; da masu ɗaukar nauyinsu da masu samar musu da makamai da masu ba su bayanan sirri da sauran masu taimaka musu, ba tare da la’akari da asalinsu ko wata alaƙarsu ba.

Masu AlakaTRT Afrika - Ana zargin Lakurawa da kashe aƙalla mutum 28 a masallaci a Sokoto

Taron, wanda gwamnatin Jihar Zamfara ta shirya, ya haɗa gwamnoni, sarakunan gargajiya, shugabannin hukumomin tsaro, ƙwararru, wakilan ƙungiyoyin fararen-hula da sauran manyan masu ruwa da tsaki daga yankin, domin tattauna matsalolin ’yanbindiga, garkuwa da mutane, yaɗuwar makamai, rikice-rikicen al’umma, rikicin manoma da makiyaya, da sauran barazanar tsaro da yankin ke fuskanta.

A jawabinsa, Disu ya jaddada cewa babu wata hukumar tsaro, gwamnati ko wata hukuma da za ta iya tabbatar da tsaron Arewa maso Yamma ita kaɗai, yana mai kira da a ƙara ƙarfafa musayar bayanan sirri, haɗin gwiwa tsakanin jihohi, gudanar da ayyukan tsaro tare, tsaron iyakoki, haɗa kai da al’umma da kuma samar da ingantattun hanyoyin bayar da gargaɗi da wuri.

Ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da sarakunan gargajiya da al’ummomin yankuna ke takawa wajen samar da sahihan bayanan sirri da kuma taimakawa wajen hana aikata laifuka.

Disu ya sake tabbatar da aniyar Rundunar ’Yansandan Nijeriya na ci gaba da gudanar da aikin ’yansanda bisa bayanan sirri, ayyukan tsaro da fasaha ke jagoranta, gaggawar kai dauki, haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da kuma haɗin kai da al’umma.