| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Patrick Vieira, tsohon ɗanwasan Arsenal ya zama sabon kocin tawagar Senegal
Senegal ta naɗa Patrick Vieira, wanda zakaran Kofin Duniya ne na 1998 a Faransa, don ya zama sabon kocin tawagar ƙasar, kamar yadda hukumar ƙwallon ƙafa ta Senegal ta sanar a ranar Talata.
Patrick Vieira, tsohon ɗanwasan Arsenal ya zama sabon kocin tawagar Senegal
Senegal ta naɗa tsohon fitaccen ɗan wasan Faransa da Arsenal Patrick Vieira a matsayin mai horarwa a ranar 18 ga watan Agusta, 2026.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Senegal ta naɗa Patrick Vieira a matsayin babban kocin babbar tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar ta maza.

Wata sanarwar hukumar ta bayyana haka ranar Talata, kimanin wata guda bayan an sallami tsohon koci, Pape Thiaw, bayan an fitar da Senegal daga gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026.

Naɗin Vieira, wanda haifaffen Senegal ne, wani “mataki ne na dabara mai nufin kawo jami’ai masu ƙwarewar ƙoli, daidai da burin harkar wasanni na ƙasarmu”, in ji hukumar cikin wani saƙo a kafafen sada zumunta.

Babban aikin Vieira zai kasance na farfaɗo da tawagar bayan Senegal ta sha kashi a hannun Belgium a zagayen ‘yan-32 na Gasar Kofin Duniya da aka kammala a watan Yuli.

Ƙasa da makonni biyu bayan hakan, an sallami koci Thiaw, wanda tsohon ɗanƙwallon ƙasar ne mai shekaru 45, wanda ya karɓi ragamar tawagar tun a shekarar 2024.

Ƙarin albashi

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Senegal (FSF), ya ce Thiaw ya nemi ƙarin albashi lokacin ana tsaka da yanayin rashin tabbas a tawagar yayin gasar Kofin Duniya.

Hukumar FSF ta tabbatar da naɗin Patrick Vieira, wanda ya girma a Faransa tun yana shekara takwas, kafin ya zama muhimmin ɗanwasa a tawagar Faransa da kuma Arsenal.

Vieira ya kasance muhimmi a Arsenal, wadda ta lashe gasar Firimiya ta Ingila sau uku tsakanin 1998 da 2004, kafin ya koma Juventus sannan Inter Milan ta Italiya.

Bayan ya yi ritaya a Manchester City, Vieira ya fara aikin horarwa a New York City FC daga 2016, kafin ya jagoranci ƙungiyar Nice a Faransa daga 2018 zuwa 2020.

Mai shekaru 50, Vieira ya koma Ingila a matsayin manajan Crystal Palace a 2021 amma an sallame shi a Maris ɗin 2023 bayan rashin nasara a wasanni 12. Daga baya ya yi gajeren aiki a Strasbourg ta Faransa, da Genoa ta Italiya.

A tawagar Faransa, ya buga wasanni 107 kuma ya lashe Kofin Duniya a 1998 tare da Faransa, da kuma gasar Euro a 2000.