Shugaban ƙasar Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahmane Tiani, ya yi wasu sauye-sauye a majalisar ministocin ƙasar ranar Talata, makonni biyu bayan wani bore da wasu sojoji suka yi a Yamai.
Kafofin watsa labaran ƙasar, ciki har da kamfanin dillancin labaran ƙasar, ANP, sun ruwaito sauye-sauyen bayan wata doka da Shugaba Tiani ya sanya wa hannu.
Dokar ta naɗa Kanal Bilaly Elhadji Gambobo a matsayin Ministan Noma da Kiwo, inda ya maye gurbin Kanal Mahaman Elhadj Ousmane.
Kazalika, Abdourahamane Oumarou ya karɓi Ma’aikatar Sake Gina Ƙasa da Bunƙasa Ɗabi’un Zamantakewa, inda ya maye gurbin Ali Ben Salah.
Shi kuma Laftanal-Kanar Seyni Alzouma aka naɗa Ministan Makamashi, yayin da Hamani Kargne ya maye gurbin Adji Ali Salatou a matsayin Ministan Sadarwa da Sabbin Fasahohin Bayanai.
A cewar ANP, gwamnatin ƙasar tana da mambobi 26 tun bayan sauyin da aka samu a tsarin gwamnati a ranar 26 ga Janairu, 2026.
Sauya babban hafsan soji
Waɗannan sauye-sauyen ministocin na zuwa ne kwanaki bayan Shugaba Tiani ya sauya babban hafsan sojin ƙasar.
A ranar 11 ga Satumba, 2026, Tiani ya naɗa Birgediya Janar Mamane Sani Kiaou a matsayin shugaban hafsan rundunar sojojin ƙasar, inda ya maye gurbin Janar Moussa Salaou Barmou.
Kiaou, wanda a baya ya kasance Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, yanzu zai jagoranci rundunar sojojin ƙasar baki ɗaya.
Haka kuma, Shugaba Tiani ya naɗa Janar Abdourahmane Abou Zataka domin maye gurbin Kiaou a matsayin Babban Hafsan Sojojin Ƙasa.
Sanarwar da ta bayyana sauyin ba ta bayyana dalilin da ya sa aka sauke Janar Barmou daga muƙaminsa ba.
Kiaou ya yi suna a matsayin kwamandan soji da ya jagoranci ayyukan yaƙi da ƙungiyoyin ’yan tawaye a yankin Tillaberi da ke yammacin Nijar, da kuma yankin Diffa a kudu maso gabashin ƙasar.
Kafofin yaɗa labaran Nijar sun kuma ruwaito cewa kafin naɗin nasa, Kiaou ya kammala rangadin wasu muhimman sansanonin soji na ƙasar, wanda aka ce an shirya shi domin ƙarfafa haɗin kai tsakanin sojoji.
Kiaou ya kuma taka rawa wajen tattaunawar da ta kai ga janye dakarun Faransa da Amurka daga Nijar bayan sauyin gwamnati na shekarar 2023.
Alaƙar Nijar da Rasha
Tun bayan juyin mulkin shekarar 2023, gwamnatin Tiani ta ƙara kusantar Rasha tare da rage alaƙarta da wasu ƙasashen Yamma, musamman Faransa, wadda ta yi wa Nijar mulkin mallaka.
A makon da ya gabata, gidan talabijin na ƙasar ya ruwaito Shugaba Tiani yana zargin Faransa da hannu a yunƙurin tawayen da aka yi a ƙarshen watan Agusta.
Faransa ta musanta zargin.
Yunƙurin bore a Yamai
A ranar 28 ga Agusta, wasu sojoji sun fara kai hare-hare kan wasu muhimman wurare a Yamai, lamarin da ya ci gaba zuwa ranar 29 ga Agusta.
Wasu daga cikin sojojin sun fake a wani muhimmin sansanin soji da ke kusa da filin jirgin saman Yamai, yayin da suke yunƙurin kifar da tsarin mulkin ƙasar.
Dakarun da ke biyayya ga gwamnati, tare da taimakon mayakan Africa Corps na Rasha, sun murƙushe boren, inda aka kashe ko kama wasu daga cikin sojojin da suka bijire wa gwamnati.
Jakadan Rasha a Nijar, Viktor Voropaev, ya tabbatar da cewa mayakan Africa Corps na Rasha sun shiga aikin murƙushe boren.
Lamarin ya kasance ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da gwamnatin Tiani ta fuskanta tun bayan da ta karɓi mulki a shekarar 2023.















