| Hausa
TATTALIN ARZIKI
3 minti karatu
Matatar Dangote ta sayar da hannayen-jarin fiye da naira biliyan 10 mintuna kaɗan bayan ƙaddamarwa
Matatar man fetur ta Dangote da ke Nijeriya ta jawo hankalin masu zuba jari inda suka sayi hannayen-jari na fiye da naira biliyan 10 mintuna kaɗan bayan buɗe sayar da hannayen-jarin ga jama’a a karon farko a ranar Litinin.
Matatar Dangote ta sayar da hannayen-jarin fiye da naira biliyan 10 mintuna kaɗan bayan ƙaddamarwa
Dangote ya buɗe kasuwar hannun-jarin da kuma bikin sayar da shi ga ‘yan kasuwa da misalin ƙarfe 9:35 na safe, agogon ƙasar, a Legas.

Matatar man fetur ta Dangote da ke Nijeriya ta jawo hankalin masu zuba jari inda suka sayi hannayen-jari na fiye da naira biliyan 10 mintuna kaɗan bayan buɗe sayar da hannayen-jarin ga jama’a a karon farko a ranar Litinin, a cewar jami’ai. Ana sa ran cinikin zai iya zama mafi girma na sayar da hannun jari ga jama'a da aka taɓa yi a Afirka.

Aigboje Aig-Imoukhuede, shugaban Access Holdings, ɗaya daga cikin manyan rukunin bankuna a Nijeriya, ya ce dubban masu zuba jari sun yi rajistar neman sayen hannun jarin cikin mintuna kaɗan bayan buɗe cinikin.

“An riga an samu buƙatun sayen hannayen-jari na biliyoyin naira daga dubban masu zuba jari cikin mintuna kaɗan ko ƙasa da awa guda,” in ji Aig-Imoukhuede yayin bikin buɗe cinikin a Nigerian Exchange (NGX) da ke Legas.

Shugaban NGX, Umaru Kwairanga, shi ma ya tabbatar da cewa an riga an yi rajistar buƙatun sayen hannun jari na fiye da naira biliyan 10 tun bayan buɗe cinikin da ƙarfe 8 na safe.

Rukunin farko na sayar da hannayen-jarin ga jama’a wanda aka fi sani da IPO, wanda zai gudana daga ranar 14 ga Satumba zuwa 13 ga Oktoba, na da burin tara dala biliyan 1.6 daga masu zuba jari a faɗin Afirka, tare da burin samun masu hannun jari har miliyan 10. Ana sa ran za a fara cinakayyar hannun-jarin matatar a kasuwar hada-hadar hannayen-jari ta Nijeriya a watan Nuwamba.

A cewar kamfanin, za a yi amfani da kuɗin da aka tara wajen faɗaɗa ƙarfin tace man matatar daga ganga 700,000 na ɗanyen mai a kowace rana a yanzu zuwa ganga miliyan 1.4 a kowace rana nan da shekarar 2030.

Masu AlakaTRT Afrika - Matatar Dangote za ta buɗe sayar da hannayen-jari na Naira tiriliyan 2.15


Matatar, wadda ke kusa da Legas, mallakin hamshakin ɗan kasuwar Nijeriya Aliko Dangote ce, kuma ta fara aiki a shekarar 2024. Idan ta kai cikakken ƙarfin aiki, ana sa ran za ta zama ɗaya daga cikin manyan matatun mai masu tsarin tacewa guda ɗaya a duniya, tare da ƙara ƙarfin Nijeriya na tace ɗanyen man da take haƙowa a cikin gida.

An kiyasta darajar Matatar Dangote a kusan dala biliyan 49 a cikin IPO ɗin. Masu nazari sun ce fara hada-hadar hannun-jarin matatar a kasuwa na iya ƙara jumullar darajar kamfanonin da ake hada-hadarsu a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Nijeriya da kusan kashi ɗaya bisa uku.

Dangote ya buɗe kasuwar hannun-jarin da kuma bikin sayar da shi ga ‘yan kasuwa da misalin ƙarfe 9:35 na safe, agogon ƙasar, a Legas, tare da manyan jami’an matatar da wakilan wasu cibiyoyin hada-hadar kuɗi na Afirka.

Rumbun Labarai
Matatar Dangote za ta buɗe sayar da hannayen-jari na Naira tiriliyan 2.15
Apple ya gabatar da iPhone Duo, wayarsa ta farko da ake rufewa
Aliko Dangote ya ƙaddamar da fara sayar da hannun-jarin matatar mansa ga jama'a
Uganda ta sanar da samun raguwar kaso 15% a hada-hadar fitar da kofi zuwa ƙasashen waje
Zuba jari a ɓangaren makamashi na Nijeriya na iya ƙaruwa cikin shekaru biyar – Hukumar IEA
Matatar Dangote ta Nijeriya za ta fara sayar da hannayen jari a karon farko nan da ‘yan kwanaki
Shirin bankin da ba ya karɓar ruwa ba don tallata wani addini ba ne – Gwamnan Babban Bankin Ghana
Trump ya soki Canada kan haraji cikin rigimar cinikayyar da Amurka ke yi da ƙasar
Kayan da Turkiyya ta fitar zuwa Afirka a 2026 sun haura na dala biliyan 13
Kuɗin Ghana ya koma fuskantar matsi, na Uganda na farfaɗowa, na Nijeriya zai iya sauyawa kaɗan
Amurka ta yi barazanar saka wa tattalin arzikin Iran takunkumin da 'duniya ba ta taɓa gani ba'
Gwamnatin Nijeriya za ta farfado da burtalan kiwo 417 a faɗin ƙasar
Za a gyara kamfanin NNPC tare da sayar da hannayen jarinsa a kasuwar hannayen jarin Nijeriya —Tinubu
Matatar Dangote ta fitar da tan fiye da 400,000 na man jiragen sama zuwa Turai a watan Yuli - Rahoto
Hukumar Kasuwanci Marar Shinge ta Afirka ta sanya hannu da wani kamfanin Nijeriya don inganta fito
A lokacin da cututtuka suka tsallaka iyaka: Manoman Afirka na neman sabbin matakan kariya
Farashin fetur a Amurka ya tashi sakamakon tsaiko a Hormuz da sanarwar Houthi ta rufe Bahar Maliya
ECOWAS ta sanya hannu kan yarjejeniyar tallafa wa aikin bututun iskar gas na Nijeriya da Morocco
Ƙungiyar EU ta sanar da sanya sabbin takunkumai kan cinikayyar zinare a Sudan
Hauhawar farashin kayayyaki a Ghana ta ƙaru a wata uku a jere da 5.3% a Yunin 2026