| Hausa
TATTALIN ARZIKI
2 minti karatu
Trump ya soki Canada kan haraji cikin rigimar cinikayyar da Amurka ke yi da ƙasar
Shugaban na Amurka ya zargi Ottawa da ƙaƙaba haraji mai yawa kan amfanin gona na manoman Amurka yayin da ƙasashen biyu ke fafatawa a wata rigimar cinikayya.
Trump ya soki Canada kan haraji cikin rigimar cinikayyar da Amurka ke yi da ƙasar
(Tsohon Hoto) Canada ta dakatar da tattaunawar cinikayya da Washington bayan Amurka ta gabatar da wasu buƙatau da Ottawa ba za ta iya lamunta ba

Shugaban Amurka Donald Trump ya soki Canada game da haraji ranar Lahadi, inda ya sabunta sukarsa kan manufofin cinikayya na Ottawa da alaƙarta da Washington.

“Canada na son fa’idar kasancewa jiha ɗaya, ba tare da kasancewa [jiha] ɗaya ba!!!” kamar yadda Trump rubuta a shafinsa na Truth Social.

Ya kuma zargi Canada da ƙaƙaba haraji mai yawa kan amfanin gonan manoman Amurka, yana mai cewa manoman Amurka sun shafe shekaru suna fuskantar “haraiji mai yawan gaske.”

Kalaman na zuwa ne cikin ce-ce-ku-cen cinikayya tsakanin ƙasashen biyu.

Daga farko, Firayimministan Canada Mark Carney ya zargi Amurka da amfani jerin sabbin haraji domin “cutar da da kuma rarraba kan” Canada, yana mai bayyana waɗannan matakan a matsayin “wani kuskure”.

Dakatar da tattaunawar cinikayya

Carney ya sha alwashin ramuwar gayya ta dala ga ko wace dala daga ranar 8 ga watan Satumba kuma ya ce Canada ta dakatar da tattaunawar cinikayya da Washington bayan Amurka ta gabatar da wasu buƙatun da Ottawa ba za ta iya lamunta ba.

Sai dai kuma wakilin cinikayya na Amurka Jamieson Greer ya ce Canada ta janye daga wata yarjejeniyar da aka kusa kammalawa wadda da za ta iya ƙara rage haraji kan kayayyakin da Canada ke fitarwa zuwa kasuwar Amurka.

Ce-ce-ku-cen ya biyo bayan matakin da Canada ta ɗauka na dakatar da tattaunawa da Amurka bisa abin da Ottawa ta bayyana a matsayin sauye-sauyen da ba za ta iya lamunta ba a cikin shawarwarin da Washington ta gabatar.