| Hausa
TATTALIN ARZIKI
2 minti karatu
Aliko Dangote ya ƙaddamar da fara sayar da hannun-jarin matatar mansa ga jama'a
Mafi ƙarancin hannun jari da mutum zai iya saya shi ne hannu 100, wanda darajarsa ta kai naira ₦52,500, sannan za a iya ƙarin hannu hamsin-hamsin.
Aliko Dangote ya ƙaddamar da fara sayar da hannun-jarin matatar mansa ga jama'a
Matatar Dangote za ta zama mafi girma a duniya bayan faɗaɗa ta zuwa ganga miliyan 1.4.

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ayyana buɗe sayar da hannun-jarin matatar mansa ga jama’ar Nijeriya a ranar Litinin 7 ga Satumban 2026.

A birnin Lagos aka yi bikin fara sayar da hannun-jarin matatar da ke da girman tace mai ganga 650,000 duk rana, wadda ke bakin tekun birnin na Lagos.

Za a sayar da hannun jarin matatar da ya kai jimillar dala biliyan 4.1 kan dala $0.000013 duk hannu, inda ake sayar da ita kan naira ₦525.

A hukumance cinikin zai fara ranar 14 ga Satumban 2026 zuwa 9 ga Oktoban 2026.

Da yake jawabi wajen bikin, Aliko Dangote ya ayyana cewa, “Abin da muke son cim mawa shi ne mu tabbatar direbobinmu, masu girki, masu hidima da kowa da kowa zai samu rabonsa a matatar.

Mafi ƙarancin hannun-jari da mutum zai iya saya shi ne hannu 100, wanda darajarsa ta kai naira ₦52,500, sannan za a iya ƙarin hannu hamsin-hamsin.

Wannan ne karo na farko da matatar ke buɗe ƙofarta ga masu zuba jari tun bayan ƙaddamar da ita a 2023, sannan tun bayan kusan shekaru 10 da aka fara gina ta kan kusan dala biliyan 20.

Kamfanin Dangote ya ce, Hukumar Kula da Hannun Jari ta Nijeriya ta amince da fara sayar da hannun jarin matatar, “wanda ake sa ran zai zama ɗaya cikin mafi girman cinikayyar hannun-jari a tarihin Nijeriya”.

Kuɗaɗen da za a tara za a yi amfani da su wajen faɗaɗa matatar, daga ganga kusan 700,000 duk rana, zuwa ganga miliyan 1.4 duk rana, wanda zai sa ta zamo matata mafi girma a duniya.