| Hausa
TATTALIN ARZIKI
2 minti karatu
Gwamnatin Nijeriya za ta farfado da burtalan kiwo 417 a faɗin ƙasar
Ministan Bunkasa Kiwon Dabbobi na Nijeriy ya ce jihohin Binuwe da Filato da Nasarawa, da Kaduna da Adamawa, da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, a matsayin wuraren da suka fi muhimmanci saboda tarihin rikice-rikicen manoma da makiyaya da ake samu.
Gwamnatin Nijeriya za ta farfado da burtalan kiwo 417 a faɗin ƙasar
Gwamnatin Nijeriya ta ware birtalai 417 da za a farfado da su don kiwon dabbobi a fadin kasar.

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da shirinta na farfaɗo da burtalan noma 417 tare da kafa sansanonin kiwon dabbobi a yankuna shida da ake yawan samun rikici a ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya.

Ministan Bunkasa Kiwon Dabbobi na Nijeriya, Idi Mukhtar Maiha ne ya bayyana hakan a ranar Talata bayan ya yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu jawabi a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Ya bayyana jihohin Binuwe, da Filato, da Nasarawa, da Kaduna da Adamawa, da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, a matsayin wuraren da suka fi muhimmanci saboda tarihin rikice-rikicen manoma da makiyaya da ake samu, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito.

Maiha ya ce gwamnati ta gano burtalai da ake kiwo guda 417 a duk faɗin ƙasar, kuma ta fara wani shiri na gwaji a Jihar Filato don gwada sabon tsarin samar da wajen killace dabbobi da nufin rage zirga-zirgar shanu.

Ya ce ma'aikatar tana tuntuɓar al'ummomin makiyaya da ƙungiyoyi kimanin 34 don tabbatar da goyon bayansu ga sauyi daga kiwon sake, zuwa kiwon dabbobin da aka tsare a waje guda.

A cewarsa, kwanan nan gwamnati ta gana da makiyaya ƙarƙashin jagorancin Babban Dattijon Kungiyar Miyetti Allah da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar, yayin wani taro da aka shirya cikin makonni biyu.

Maiha ya ce kiwon dabbobi da ke yawo ko’ina ya zama tsarin da ba za a iya jurewa ba saboda hanyoyin kiwo sun ɓace sakamakon noma, da bunƙasar birane da haɓaka ababen more rayuwa.

Ya ƙara da cewa, gwamnati za ta haɓaka kiwo don kasuwanci, ta yadda za a bar ciyawa a cikin matsugunan dabbobi ko a girbe ta a wani wuri a kai ta ga dabbobin.

Ministan ya kuma ci gaba da cewa inganta nau'in kiwon zai bai wa makiyaya damar riƙe dabbobi kaɗan amma masu amfani, da rage matsin lamba a ƙasa, yayin da ake ƙara samar da madara da nama, yana mai jaddada yadda tsarin kiwo na zamani na kawo ci-gaba ga al’umma, da haɓaka tattalin arziki, da makarantu, da asibitocin dabbobi, da madatsun ruwa, da asibiton kula da lafiya da ma makamashi mai aiki da hasken rana.

Rumbun Labarai
Kayan da Turkiyya ta fitar zuwa Afirka a 2026 sun haura na dala biliyan 13
Kuɗin Ghana ya koma fuskantar matsi, na Uganda na farfaɗowa, na Nijeriya zai iya sauyawa kaɗan
Amurka ta yi barazanar saka wa tattalin arzikin Iran takunkumin da 'duniya ba ta taɓa gani ba'
Za a gyara kamfanin NNPC tare da sayar da hannayen jarinsa a kasuwar hannayen jarin Nijeriya —Tinubu
Matatar Dangote ta fitar da tan fiye da 400,000 na man jiragen sama zuwa Turai a watan Yuli - Rahoto
Hukumar Kasuwanci Marar Shinge ta Afirka ta sanya hannu da wani kamfanin Nijeriya don inganta fito
A lokacin da cututtuka suka tsallaka iyaka: Manoman Afirka na neman sabbin matakan kariya
Farashin fetur a Amurka ya tashi sakamakon tsaiko a Hormuz da sanarwar Houthi ta rufe Bahar Maliya
ECOWAS ta sanya hannu kan yarjejeniyar tallafa wa aikin bututun iskar gas na Nijeriya da Morocco
Ƙungiyar EU ta sanar da sanya sabbin takunkumai kan cinikayyar zinare a Sudan
Hauhawar farashin kayayyaki a Ghana ta ƙaru a wata uku a jere da 5.3% a Yunin 2026
Wa yake amfana a lokacin da tattalin arzikin duniya ke ci da wuta sakamakon yaƙi?
Abubuwan da dalar Amurka Tiriliyan 1.1 mallakin Elon Musk za ta iya yi a Afirka
Elon Musk ya zama tiriloniya na farko a tarihin duniya
An zargi matatar mai mafi girma a Afirka da ƙoƙarin yin babakere game da man Nijeriya
Biliyoyin kudi da gangunan mai: Yadda matatar mai ta Dangote ke ƙarfafar Afirka da makamashi
China ta faɗaɗa janye haraji baki ɗaya ga kayan da ta shigar daga ƙasashen Afirka 53
Wasu daga waje na ƙoƙarin daƙile ci-gaban Afirka, in ji  Dangote
Ghana ta bai wa wani kamfanin ƙasar lasisin haƙar zinare kan $1bn
Shigar kuɗaɗe daga waje cikin Nijeriya don zuba jari ta ƙaru da kusan kashi 90% a 2025 – Hukumomi