| Hausa
SIYASA
2 minti karatu
Sanatan Amurka ya yaba cika shekaru 100 na alaƙar Turkiyya da Amurka
Chris Coons ya bayyana cewa ‘zuzzurfar alaka da kawance masu muhimmanci’ tsakanin Amurka da Turkiyya a shekaru 100 da suka gabata sun kara dunkulewa da kasuwanci.
Sanatan Amurka ya yaba cika shekaru 100 na alaƙar Turkiyya da Amurka
Coons ya ce taron NATO da aka gudanar a Ankara ya taka rawa ta musamman da cigaban alakar a nan gaba. / AA Archive

Sanata Chris Coons na Amurka ya yi tsokaci kan dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da Amurka, yana mai cewa dangantakar kasuwanci da sana’o’i sun taimaka wajen karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.

Coons ya gabatar da jawabi a ranar Litinin a taron "Shekaru 100 na Abota" da aka gudanar a birnin New York, wanda shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da uwargidansa Emine Erdogan suka halarta.

Ya bayyana dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu a matsayin "shekaru 100 na zumunci mai zurfi da ma'ana, wanda kasuwanci ya karfafa."

Da yake magana kan ziyarar da ya kai Ankara kwanan nan don halartar taron NATO, Coons ya yi tsokaci kan kawancen NATO na kasashen, yana mai cewa a shekara mai zuwa Turkiyya da Amurka za su cika shekaru 75 a matsayin kawaye a NATO.

Gudunmawa masu muhimmanci

Yayin da yake magana kan muhimman gudunmawar da 'yan kasuwar Turkiyya ke bayarwa a Amurka, Coons ya bayyana cewa taron kolin kungiyar NATO da aka gudanar a Ankara shi ma ya taka muhimmiyar rawa wajen karfafa makomar kawancen.

Taron bikin cika shekaru 100 na zumunci, wanda Kungiyar 'Yan Kasuwa ta Amurka da Majalisar Kasuwanci ta Amurka da Turkiyya (USTBC) suka shirya tare da karbar bakuncin Shugaban Majalisar Hamdi Ulukaya a birnin New York, ya samu halartar Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, Ministan Baitulmali da Kudi Mehmet Simsek, Ministan Ciniki Omer Bolat, Ministan Makamashi da Albarkatun Kasa Alparslan Bayraktar, Ministan Masana'antu da Fasaha Mehmet Fatih Kacir, Ministan Lafiya Kemal Memisoglu, da kuma Ministar Iyali da Ayyukan Jama'a Mahinur Ozdemir Goktas.

Haka kuma, taron ya samu halartar Mehmet Oz, shugaban cibiyar kula da shirye-shiryen magumguna da tallafin magunguna, tare da manyan jami'an gwamnatin Amurka da dama da kuma 'yan majalisar dokokin kasar.

Rumbun Labarai
Duk wanda ke alƙawarin dawo da tallafin mai yana yaudarar 'yan Nijeriya ne — Abdulaziz Yari
Nijar ta ce sojoji 'yantawaye ne suka ƙaddamar da hare-hare a babban birnin ƙasar Yamai
Tinubu da gwamnoni na neman rage farashin sufuri wa 'yan Nijeriya daga ranar 1 ga Oktoba
Tufka da warwarar Atiku kan tallafin mai na nuna cewa siyasa kawai yake da batun tallafin— Gwamnati
Maishari'ar Amurka ta soke umarnin Trump na haramta wa 'yan Nijeriya da 'yan ƙasashe 74 biza
Ƙiyayyar da ake nuna wa musulmi El-Sayed ta ƙaru bayan ya lashe zaɓen fid da gwani a Amurka
Ƙungiyar Tarayyar Turai ta musanta janyewa daga aikin sa ido a zaɓen Nijeriya na 2027
Cutar kansa ta yadu sosai a jikin tsohon Shugaban Amurka Biden, in ji dansa
Tinubu ya umarci EFCC ta nemi kotu ta sake buɗe asusun gwamnatin Jihar Osun
Yadda rikicin Hormuz ke amon ra’ayin Ibn Khaldun game da yanayin ƙasa da ƙarfin iko
Yarjejeniyar nukiliyar Amurka da Saudiyya ta sauya ƙa'idojin yanayin siyasa a Gabas ta Tsakiya
Kotun Daukaka Kara ta soke hukuncin kotun da ta yi umarnin soke rajistar ADC a Nijeriya
Tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ta rushe. Ta yaya sabon rikicin ya fara?
An ja labulen babban taron Ankara: Me ya rage wa NATO?
Shugabannin NATO sun buɗe rana ta ƙarshe a Ankara da mayar da hankali kan Arctic, Iran da Ukraine
Trump ya ce tsagaita wuta da Iran ta zo ƙarshe bayan sabbin hare-hare, amma tattaunawa za ta ci gaba
Kar ku auna ƙawaye a NATO da kuɗaɗen da suke kashewa, ku auna su da me suke ginawa
Bayani dalla-dalla: Shin kotu ta soke rajistar jam'iyyar NDC ne a Nijeriya?
Bayan shekaru 22, Taron NATO ya dawo Ankara a wata duniya ta daban
Shugaba Tinubu ya ce Nijeriya na cikin jarabawa amma za ta warware lafiya