| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Birtaniya za ta bai wa Saudiyya 'kariyar' soji don daƙile hare-haren 'yan Houthi
Birtaniya ta tura jirgin ba da mai a sama domin bai wa jiragen saman Saudiyya damar shan mai yayin da hare-haren 'yan Houthi ke barazana ga safarar jiragen ruwa na masarautar da ma yankin baki ɗaya.
Birtaniya za ta bai wa Saudiyya 'kariyar' soji don daƙile hare-haren 'yan Houthi
Wani jirgin sojin saman Birtaniya na shan mai a yayin wnai aiki a Gabas Ta Tsakiya. (Tsohon: Hoto) /

Firaministan Birtaniya Andy Burnham ya tabbatar da cewa ƙasarsa ta amince ta ba da taƙaitaccen tallafin soji ga Saudiyya domin daƙile hare-haren Houthi.

Burnham ya shaida wa manema labarai da ke jirginsa zuwa babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya a New York cewa ya amince rundunar sojin saman Birtaniya ta ba da damar shan mai a sama ga jiragen saman Saudiyya.

Yarjejeniyar ta wucin-gadi an tsara ta ne ta wasu makonni, duk da cewa Burnham ya ce za a iya sabunta ta.

Jami’an Birtaniya sun tabbatar da cewa za a fara aikin a cikin kwanaki masu zuwa, inda za a tura jirgin ba da mai a sama samfurin RAF Voyager domin bai wa jiragen Saudiyya damar shan mai domin ayyukan "kariya" .

"Ina aiki ne domin kare muradun Birtaniya da kuma yankin gaba ɗaya domin Saudiyya wadda ta kasance tana fama da hare-hare tana fuskantar yiwuwar ƙarin dagulewar lamura, kuma muna buƙatar mu tabbatar da cewa waɗannan hanyoyin suna buɗe," kamar yadda Burnham ya bayyana, yana mai magana game da muhimman hanyoyin jigilar mai ta teku.

Rikici na yanki

Yaƙe-yaƙe cikin Yemen sun sake ɓarkewa sosai a baya bayan nan, inda ‘yan Houthi suke ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jirage mara matuƙa zuwa cikin ƙasar Saudiyya, ciki har da wani harin da aka kai Riyadh a ranar Asabar wanda tsarin tsaron sararin samaniya ya kakkaɓo.

‘Yan Houthi sun bayyana cewa sun yi ƙawanya kan wucewar jiragen ruwan Saudiyya a Bahar Ahmar da kuma Mashigar Bab al Mandab— wata tsukakkiyar hanya da ke ɗaukar kashi 12 cikin 100 na kasuwancin duniya— inda suke kai hari kan jiragen ruwa na ‘yankasuwa da kuma kayayyakin makamashi a cikin masarautar.

Daga farko a wannna watan, ‘Yan Houthi sun fito ta ɓangarorin gaɓar teku, inda suka kama muhimmiyar tashar jiragen ruwa ta Mokha da kuma muhimmin tsibiran Bahar Ahmar, lamarin da ya bai wa ƙungiyar ƙarin ikon leƙen asiri kan tafiya ta ruwa.

Yayin da take Allah Wadai da hare-haren, Landan ta jaddada jajircewarta ga "aiki da abokan aiki domin tallafa wa zaman lafiyar yankin da kare fararen-hula da kuma taimaka wa damar tafiya ta aikin jinƙai."

Yayin da gwamnatocin Amurka na baya suka kai hare-hare kai-tsaye kan ‘yan Houthi, Washington ta nuna cewa ba ta son ɗaukar matakin soji a rikicin na baya bayan nan.

Tura jirgin ya biyo bayan rahotannin da ke cewa Riyadh ta nemi tallafin tsaron sama a hukumance ne daga abokan tarayya na ƙasa da ƙasa ciki har da Birtaniya da Faransa da Masar da Pakistan domin daƙile hare-haren makamai masu linzami da na jirage mara matuƙa.