A Jihar Filato da ke yankin tsakiyar Nijeriya an samu kimanin mutum 11,000 da suka kamu da cutar tarin fuka (TB) a shekarar 2026. An gano marasa lafiya 2,047 tare da fara ba su magani tsakanin watan Yuli da Satumba, kamar yadda wani jami’in lafiya ya bayyana.
Yohanna Bot, jami’in sa ido da tantance sakamakon shirin yaƙi da cutar tarin fuka na jihar, ne ya bayyana waɗannan alkaluma a wani taron wayar da kan kafafen yaɗa labarai da aka gudanar a Jos, babban birnin jihar, a yammacin ranar Lahadi.
A cikin wata sanarwa da ya aikewa kamfanin dillancin labarai na Anadolu, Bot ya ce an ƙididdige yawan masu cutar ne bisa hasashen cewa akwai mutane 219 masu cutar a cikin kowane mutum 100,000. Ya ƙara da cewa ana ba marasa lafiyar da aka gano magani a cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban a faɗin jihar.
Ya danganta yaɗuwar cutar tarin fuka da yadda take yaɗuwa ta iska, cunkoson jama’a, rashin ingantaccen abinci mai gina jiki da kuma raunin garkuwar jiki. Ya kuma bayyana cewa yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar da tsofaffi na cikin waɗanda suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar.
Fahimta marar kyau game da cutar
Jami’in ya kuma yi gargaɗin cewa kyama da kuma fahimta marar kyau game da cutar na hana wasu mazauna yankin neman kulawar likita a kan lokaci.
Ya ce har yanzu wasu mutane na danganta cutar tarin fuka da abubuwan da suka shafi ruhi ko kuma tsafe-tsafe.
Rashin tsaro da tilasta wa mutane barin muhallansu sun ƙara dagula ƙoƙarin gano masu cutar da kuma ba su magani, musamman a ƙananan hukumomin Mangu, Jos ta Kudu da Barkin Ladi, inda tashe-tashen hankula suka tilasta wa mazauna yankin komawa sansanonin ‘yan gudun hijira a cikin ƙasarsu.
Bot ya ce ma’aikatan lafiya na ba da fifiko ga kai ziyara cikin al’umma da kuma gudanar da gwaje-gwaje domin gano masu cutar tun da wuri a sansanonin ‘yan gudun hijira da cibiyoyin gyaran hali.
Ya kuma nuna damuwa kan ƙarancin magungunan cutar tarin fuka, inda ya danganta matsalar da tangardar hanyoyin samar da magunguna da kuma dogaro sosai da tallafin kuɗi daga ƙasashen waje, musamman tallafin Asusun Tallafa wa Yaƙi da AIDS, Tarin Fuka da Zazzabin Cizon Sauro na Duniya (Global Fund).
Nijeriya na ci gaba da kasancewa cikin ƙasashen duniya da ke da yawan masu fama da cutar tarin fuka.
Ana iya kare kai daga cutar tarin fuka kuma ana iya warkar da ita. Sai dai jinkirin gano cutar, ƙarancin damar samun magani da kuma kyamar da al’umma ke nuna wa masu cutar na ci gaba da zama manyan ƙalubale ga ƙoƙarin daƙile yaɗuwarta.

























