| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
An dakatar da Cristiano Ronaldo na tsawon kwana 30 da cin sa tarar €255 kan barin sansanin Portugal
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Portugal ta dakatar da Cristiano Ronaldo na tsawon kwanaki 30 bayan ya bar sansanin tawagar ƙasar sakamakon saɓani da ya samu da koci Jorge Jesus kan rawar da zai taka a cikin tawagar.
An dakatar da Cristiano Ronaldo na tsawon kwana 30 da cin sa tarar €255 kan barin sansanin Portugal
An dakatar da Cristiano Ronaldo na tsawon kwana 30 da cin sa tarar €255 kan barin sansanin Portugal

An dakatar da Cristiano Ronaldo na tsawon kwanaki 30, tare da cin sa tarar yuro 255, kwatankwacin naira 381,000 kan barin sansanin tawagar Portugal.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Portugal ta dakatar da Cristiano Ronaldo na tsawon kwanaki 30 bayan ya bar sansanin tawagar ƙasar sakamakon saɓani da ya samu da koci Jorge Jesus kan rawar da zai taka a cikin tawagar.

Kwamitin ladabtarwa na hukumar ya ce ya tabbatar da laifin da ake zargin ɗanwasan mai shekaru 41 da aikatawa, tare da ci tararsa Yuro 255 kwatankwacin naira 381,000.

Ronaldo ya bar sansanin Portugal da ke birnin Copenhagen kafin wasan ƙasar da Denmark a Gasar Nations League a farkon wannan watan.

Hakan ya biyo bayan zargin da ya yi na cewa Jesus ya karya alkawari sau biyu dangane da rawar da zai taka, bayan da aka ajiye shi a benci ba tare da ya shiga wasa ba a karawar da Portugal ta yi da Norway.

Jesus ya musanta cewa ya yi wata yarjejeniya da Ronaldo, amma ya nuna cewa har yanzu akwai damar ɗanwasan ya koma tawagar bayan nasarar da Portugal ta samu da ci 2-1.

Sashen kwamitin ladabtarwa da ke kula da harkokin da ba na ƙwararru ba ya ce Ronaldo ya aikata laifin da gangan, wanda ya saɓa wa sashe na 160(1) na ƙa’idojin ladabtarwa na hukumar.

An fara binciken lamarin ne a ranar 9 ga Oktoba, bayan rahotannin da aka bayar kwanaki biyu kafin hakan.

Sai dai sanarwar hukumar ba ta fayyace wasannin ko ayyukan da dakatarwar za ta shafa ba, ko kuma ko za a ƙirga lokacin da Ronaldo ya riga ya yi a ƙarƙashin dakatarwar wucin gadi cikin kwanaki 30 ɗin.

Daga baya, Ronaldo ya nemi afuwa kan rashin gaisawa da magoya baya bayan wasan Norway da kuma barin abokan wasansa. Ya ce har yanzu yana shirye ya wakilci Portugal bayan ya kammala hukuncin da za a yanke masa kan lamarin.

Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Portugal, Pedro Proença, ya bayyana cewa dukkan waɗanda ke cikin hukumar suna son Ronaldo ya koma tawagar ƙasar da zarar an warware matsalar.