Hukumar tsaro ta farin kaya a Nijeriya DSS ta gurfanar da mutum biyar da ake zargi da hannu a garkuwa da masu yi wa ƙasa hidima (‘yan NYSC) 20 tare da wani farin hula ɗaya a kan babbar hanyar Owerri zuwa Onitsha a jihar Imo.
A babbar kotun jihar da ke Owerri ne ake sauraron ƙarar bayan ‘yansanda sun kama waɗanda ake zargin yayin wani samame da aka yi bisa bayanan sirri a jihohin Ribas da Abia tsakanin 10 zuwa 14 ga watan Oktoba.
An yi garkuwa da masu yi wa ƙasa hidiman ne a cikin sanyin safiyar ranar 1 ga watan Oktoba bayan ‘yanbindiga sun far ma wata motar bas mai ɗauke mutum 18 da ke tafiya da fasinjoji daga Ibadan, babban birnin jihar Oyo, zuwa sansanonin horar da masu yi wa ƙasa hidima a jihohin Abia da Akwa Ibom, kuma suka kora su daji.
An kai harin ne kusa da Umunoha a ƙaramar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo da misalin ƙarfe 6:30 na safiya.
A wancan lokacin mai magana da yawun rundunar ‘yansanadan jihar Imo, Henry Okoye, ya ce an ceto 10 daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin nan take, yayin da ake ci gaba da aikin bincike da ceto don gano waɗanda aka yi awon gaba da su.
Garkuwa da masu yi wa ƙasa hidiman ya ƙara jan hankalin jama’ar ƙasar bayan masu garkuwa da mutane sun tuntuɓi iyalan waɗanda aka sata suna neman kuɗin fansa da ya kai naira biliyan daya, inda suka ba su sa’o’i 24 su biya kudin.
Daga bayan suka rage kuɗin fansan zuwa naira miliyan biyar kan ko wane mutum, lamarin da ya mayar da jumullar kuɗin naira miliyan 100 kan dukkan masu yi wa ƙasa hidiman 20.
A ranar 7 ga watan Oktoba, wata runduna ta haɗin gwiwa ta jami’an DSS da sojoji da ‘yansanda sun ceto waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin a cikin dajin Amakohia-Ubi a jihar Imo bayan bincike babu ƙaƙƙautawa. Daga baya aka yi wa waɗanda aka sata din magani.
Mayar da kuɗin fansa
Sai dai kuma, Alirat Wahab, uwa ga ɗaya daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin, ta bayyana wa News Central Television cewa iyalinta ya biya naira miliyan 6 domin fanso ɗanta, wani iƙirari da ya sha bamban da yadda jami’an tsaro suka bayyana ceto masu yi wa ƙasa hidiman.
Wahab da mijinta, Obasanjo, daga bayan sun bayyana cewa an mayar musu da kuɗin da iyalinsu ya tara kuɗin fansan
Biyo bayan ceto waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin, jami’an tsaro sun ci gaba da ƙoƙarin gano da kuma kama waɗanda suka kai harin.
An kama mutum biyar da ake zargi da hannun aikata laifin yayin wasu jerin samame da aka yi a Port Harcourt, jihar Ribas da Aba, jihar Abia, tsakanin ranakun 10 zuwa 14 ga watan Oktoba.
Aikin ya haɗa da wata runduna ta haɗin gwiwa da hukumar DSS ta jagoranta, wadda ke aiki da jam’an soji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro.
Saura mutum uku da ake zargin sun tsere yayin samamen da raunin harbin bindiga in ji rahotanni.
Daga baya ne aka ƙaddamar da aikin neman su da sauran waɗanda da ake zargi da kasancewa cikin dabar garkuwa da mutanen.





















