| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
An sauke DPO kan zargin 'yan kungiyar asiri sun gyara ofishin 'yansanda a Nijeriya
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ofishin ‘yansanda na Abuloma, wanda ake zargin waɗannan mutane sun gyara kafin su kai ziyara wurin a ranar Alhamis, 15 ga Oktoban 2026, domin murnar kammala aikin.
An sauke DPO kan zargin 'yan kungiyar asiri sun gyara ofishin 'yansanda a Nijeriya
Jami’an da abin ya shafa su ne DPO da ke kula da sashen Abuloma, da kuma jami’in da ke kula da ofishin ‘yansanda na Abuloma.

Hukumomin ‘yansanda a Jihar Rivers da ke kudancin Nijeriya sun cire wasu manyan jami’ai biyu daga mukamansu sakamakon zargin cewa wasu da ake zargin mambobin ƙungiyoyin asiri ne sun gyara wani ofishin ‘yansanda, sannan suka kai ziyara wurin domin bikin kammala aikin.

Rundunar ‘Yansandan Jihar Rivers ta kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin, wanda ya ja hankalin jama’a bayan wani rahoto da ya yaɗu a shafukan sada zumunta da kuma wani bidiyo da ake yaɗawa.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ofishin ‘yansanda na Abuloma, wanda ake zargin waɗannan mutane sun gyara kafin su kai ziyara wurin a ranar Alhamis, 15 ga Oktoban 2026, domin murnar kammala aikin.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar ‘yansanda, ASP Agabe Kaborlo, ya sanya wa hannu a madadin Kwamishinan ‘Yansandan jihar, CP Olugbenga Adepoju, rundunar ta ce an nemi jami’an biyu su bayar da bayanin abin da ya faru, sannan aka cire su daga mukamansu har sai an kammala bincike.

Jami’an da abin ya shafa su ne DPO da ke kula da sashen Abuloma, da kuma jami’in da ke kula da ofishin ‘yansanda na Abuloma.

Rundunar ta yi Allah wadai da duk wani aiki ko alaƙa da za ta iya lalata mutunci, ladabi da ƙa’idojin aikin ƙwararru na Rundunar ‘Yansandan Nijeriya.

Ta yi gargaɗin cewa bai kamata a mayar da ofisoshin ‘yansanda, waɗanda cibiyoyin gwamnati ne da aka kafa domin kare ’yan ƙasa da tabbatar da bin doka, wuraren da ƙungiyoyin da ake zargi da aikata laifuka za su yi amfani da su wajen neman karɓuwa ko halaccin jama’a ba.

Haka kuma, ‘yansandan sun sake jaddada matsayarsu na rashin lamuntar aikata laifuka ko duk wani hali da zai iya raunana amincewar jama’a ga hukumomin tabbatar da doka.

Kwamishinan ‘yansandan ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin yadda lamarin ya faru da kuma tabbatar da sahihancin zarge-zargen.