| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Wannan damuwa na iya kawo cikas ga yaƙi da cutar, musamman ganin cewa rashin amincewar jama’a da ma’aikatan lafiya da hukumomin da ke aikin shawo kan cutar na daga cikin manyan ƙalubalen dakile yaɗuwarta.
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
HOTON TARIHI: Ma'aikatan lafiya na ɗauke da gawar wani da cutar Ebola ta kashe a Bunia, lardin Ituri, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.

Babbar hukumar kula da lafiyar jama’a ta Afirka, Africa CDC, da hukumomin lafiya na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun yi kira da a ƙara bayyana yadda ake amfani da kuɗaɗen yaƙi da cutar Ebola.

Hukumomin sun ce bayanan kuɗaɗen da ƙungiyoyin agaji suka gabatar sun nuna cewa har yanzu ba a yi cikakken bayani kan yadda aka yi amfani da sama da dala miliyan 700 na kuɗaɗen tallafi ba.

Wannan damuwa na iya kawo cikas ga yaƙi da cutar, musamman ganin cewa rashin amincewar jama’a da ma’aikatan lafiya da hukumomin da ke aikin shawo kan cutar na daga cikin manyan ƙalubalen dakile yaɗuwarta.

A baya, an sha samun zarge-zargen nuna son kai da cin hanci da rashawa a ayyukan yaƙi da Ebola a Kongo.

Babban daraktan Africa CDC, Dr Jean Kaseya, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar Alhamis cewa lokaci bai yi da za a ce an karkatar da kuɗaɗen ba. Sai dai ya bayyana gibin da ke cikin bayanan a matsayin babbar matsala ta rashin gaskiya da cikakken rahoton kuɗaɗe, wadda ta hana hukumomi samun cikakken bayani kan kuɗaɗen da aka tara da waɗanda aka kashe.

Ana barazanar hana wasu ƙungiyoyi aiki a Afirka

Kaseya ya ce ƙasashen da ke bayar da tallafi sun tura kusan dala miliyan 962 ga ƙungiyoyin da ke aiwatar da ayyukan yaƙi da Ebola a Kongo, maimakon su ba gwamnatin ƙasar kai tsaye.

Ya ƙara da cewa ƙungiyoyin da suka halarci wani taron baya-bayan nan da Ma’aikatar Lafiya ta Kongo ta shirya, waɗanda suka kai kusan kashi ɗaya bisa uku na dukkan ƙungiyoyin da ke gudanar da ayyukan, sun gabatar da bayanan kuɗaɗensu.

A cewarsa, waɗannan ƙungiyoyi sun ce sun karɓi dala miliyan 228, sun kashe dala miliyan 127, yayin da kusan dala miliyan 100 ke nan a hannunsu.

Ministan Lafiyar Kongo, Samuel-Roger Kamba, ya goyi bayan wannan kira a wani saƙo da ya wallafa a shafin X a daren Alhamis. Ya ce wajibi ne ƙungiyoyin agaji su gabatar wa ma’aikatarsa da bayanai kan tushen kuɗaɗensu, manufofin tallafin da kuma matakin aiwatar da ayyukansu.

Kaseya ya yi gargaɗin cewa za a iya hana ƙungiyoyin da suka ƙi bin ƙa’idojin aiki a Kongo, tare da saka su cikin jerin ƙungiyoyin da aka haramta wa aiki a faɗin Afirka.