Shugaban ƙasar Masar Abdel Fattah Al-Sisi a ranar Asabar ya bayyana cewa wa’adinsa na shugabancin ƙasar zai ƙare a shekarar 2030, yana mai jaddada cewa ba za a yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima domin tsawaita wa’adinsa ba, a cewar jaridar gwamnatin ƙasar ta Al-Ahram.
“Shekarar 2030 ce za ta kawo ƙarshen wa’adina na shugabancin ƙasa. Wannan batu ya riga ya kammala,” in ji Sisi yayin bikin yaye ɗalibai a Kwalejin Sojojin Masar da ke Sabon Babban Birnin Gudanarwa.
Sisi, wanda aka sake zaɓa a shekarar 2023 domin wa’adin mulki na shekaru shida bayan samun kusan kashi 90 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, ya ce “ba za a taɓa kundin tsarin mulkin Masar ba,” yana mai jaddada muhimmancin hana duk wani saɓa wa ƙa’idojin kundin tsarin mulki da dimokuraɗiyya.
Ya ce kundin tsarin mulkin ya fayyace rawar da rundunar sojin ƙasar ke takawa wajen kare tsarin mulki, dimokuraɗiyya da muhimman ginshiƙan ƙasa.
Ya yi alƙawarin kare Saudiyya
“Ba zan bar ƙasar Masar ba har sai ta cika da ’yan ƙasarta waɗanda za su iya ɗaukar nauyin gudanar da al’amuranta,” in ji shi, yana mai cewa a halin yanzu ana horas da sabbin shugabanni na sabon ƙarni a Kwalejin Sojojin Masar.
Sisi ya kuma bayyana cewa Masar a shirye take ta ɗauki duk matakan da Saudiyya za ta buƙata domin kare tsaron ƙasar da kuma ikon mulkinta.
“Za mu ɗauki duk matakin da ya dace domin kare Saudiyya,” in ji shi, yana mai cewa zai buƙaci majalisar dokokin ƙasar ta gudanar da zaman gaggawa domin ba da izinin ɗaukar irin waɗannan matakai idan Saudiyya ta buƙata.
“Mun tsaya tsayin daka wajen kare yankunan ’yan’uwanmu na ƙasashen yankin Tekun Fasha,” in ji shi.




















