| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Nijar ta ayyana mummunan haɗarin muhalli bayan malalar mai
Bidiyon da aka watsa a a labaran yamma ya nuna yadda ɗanyen mai ke ɓulɓula sama na tsawon mitoti .
Nijar ta ayyana mummunan haɗarin muhalli bayan malalar mai
Nijar ta ayyana mummunan haɗarin muhalli bayan malalar mai

Wani gagarumin malalar ɗanyen mai da iskar gas daga rijiyar mai a hamadar gabashin Nijar ya haddasa wani mummunan haɗarin muhalli, kamar yadda Ma’aikatar Man Fetur ta ƙasar ta sanar a ranar Litinin.

Nijar, ƙasa da ba ta kusa da teku a Yammacin Afirka, ta fara haƙo mai a shekarar 2011. A yanzu tana haƙowa da tace dubban ganga na mai a kowace rana, musamman a yankin Agadem.

A fannin man fetur, irin wannan lamari na faruwa ne idan mai da iskar gas suka fita daga rijiyar ba tare da an iya shawo kan malalar ba. Wannan na iya haddasa babbar illa ga muhalli, amma ba lallai ne yana nufin fashewa ta auku ba.

A cewar sanarwar ma’aikatar da aka karanta a gidan talabijin na ƙasa, lamarin ya faru ne a rijiyar mai ta Goumeri W8 a ranar 25 ga Satumba. Rijiyar tana da nisan kusan kilomita 1,700 daga Yamai, babban birnin ƙasar.

Illar da lamarin ya yi wa muhalli

Sanarwar ta bayyana lamarin a matsayin “mummunan haɗarin muhalli na musamman”, wanda ya haɗa da fitar ɗimbin ɗanyen mai da iskar gas zuwa sama, har tsayin da ya haura mita 10.

Hotunan da aka nuna a labaran yamma sun nuna ɗanyen mai na kwarara zuwa sama da ƙarfi, yayin da malalar ta bazu a ƙasa na tsawon daruruwan mita.

Ma’aikatar ta ce ya zuwa ranar Litinin, an samu nasarar shawo kan lamarin a wani ɓangare, amma har yanzu ba a iya sarrafa shi gaba ɗaya ba.

Ta ƙara da cewa har yanzu ba a gano musabbabin faruwar lamarin dalla-dalla ba, amma an kawar da zargin cewa masu aikata laifuka ko ’yan ta’adda ne suka haddasa shi.

Ana gudanar da bincike kan lamarin tare da taimakon ƙwararru daga Aljeriya, a cewar ma’aikatar.

Kamfanin CNPC Niger Petroleum ne ke kula da rijiyar. Kamfanin wani reshe ne na kamfanin mai na ƙasar Sin mallakar gwamnati, wato China National Petroleum Corporation.

Sojoji ne ke mulkin Nijar tun bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar 2023. Wata ƙungiya mai ɗauke da makamai da ke adawa da gwamnatin sojin ta riƙa kai hare-hare lokaci-lokaci kan bututun mai mai tsawon kilomita 2,000 da ake amfani da shi wajen jigilar ɗanyen man Nijar zuwa ƙasar Benin, maƙwabciyarta mai gabar teku.