Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya karɓi kwafin daftarin kasafin kuɗin Majalisar Ɗinkin Duniya na shekarar 2027 daga hannun wakilin dindindin na Nijeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim.
Ibrahim, wanda shi ne shugaban kwamitin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da harkokin kasafin kuɗi da gudanarwa, ya miƙa wa shugaban ƙasar kasafin a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Da yake magana da ’yan jarida bayan miƙa kasafin, Ibrahim ya bayyana lamarin a matsayin mai tarihi, yana mai cewa wannan shi ne karo na farko cikin shekaru 66 da shugaban Nijeriya ya karɓi daftarin kasafin kuɗin Majalisar Ɗinkin Duniya ta wannan hanya.
Ya ce: “Wannan shi ne miƙa daftarin kasafin kuɗin Majalisar Ɗinkin Duniya na shekarar 2027, wanda Babban Zauren Majalisar da Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya suka miƙa mini domin gabatarwa ga Kwamitin Biyar. Kasafin kuɗin yana da kundi bakwai.
“Saboda haka, dole ne a miƙa shi ga ƙasata, domin ƙasata mamba ce a Majalisar Ɗinkin Duniya. Ina wakiltar kasafin kuɗin a kwamitin, don haka abin da ya dace shi ne in dawo da shi gida in miƙa wa shugaban ƙasa.
“Wannan shi ne karo na farko cikin shekaru 66 da Nijeriya za ta gabatar da kasafin kuɗi a wannan kwamiti. Karo na farko kenan. Don haka, ban san lokacin da za mu sake yin irin wannan abu a tarihi ba.”
Ibrahim ya ƙara da cewa: “Shugaba Bola Tinubu yana kafa tarihi ta hanyar karɓar wannan kasafin kuɗi, kasancewarsa shugaban ƙasa na farko cikin shekaru 66 da zai karɓi irin wannan kasafin kuɗi daga Majalisar Ɗinkin Duniya. Ba ƙaramin abu ba ne ga ƙasa ta karɓi cikakken kasafin kuɗin Majalisar Ɗinkin Duniya.”
Ya ce daftarin kasafin kuɗin ya shafi ayyukan yau da kullum na ƙungiyar da kuma ayyukan wanzar da zaman lafiya. Ya bayyana cewa an ware kusan dala biliyan 3.4 domin kasafin ayyukan yau da kullum, yayin da aka ware dala biliyan 8.5 domin ayyukan wanzar da zaman lafiya.
Ibrahim ya ce jimillar kasafin kuɗin ta kai kusan dala biliyan 14, duk da cewa alkaluman da ya ambata na waɗannan ɓangarori biyu sun haɗu sun kai dala biliyan 11.9.
Ya jaddada cewa takardar daftari ce kawai, kuma ƙasashe mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya ba su amince da ita a hukumance ba tukuna.
Da aka tambaye shi irin tallafin da Nijeriya za ta iya samu daga Majalisar Ɗinkin Duniya, Ibrahim ya ce ana ci gaba da tattaunawa kan daftarin kasafin kuɗin, amma ya ƙi bayyana takamaimai irin amfanin da Nijeriya za ta samu.
Ya kuma kawo misalin gina cibiyar taron Majalisar Ɗinkin Duniya a Kenya, wadda ta lakume dala miliyan 267, a matsayin misalin yadda ƙungiyar ke zuba jari wajen samar da ababen more rayuwa a ƙasashe mambobinta.




















