| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Nijeriya ta bayar da wa’adin mako biyu don bincike kan mutuwar mutum 37 a hannun NSCDC
Kazalika aikin kwamitin ya haɗa da tabbatar da ko akwai sakaci da aikata ba daidai ba da haɗin baki ko keta doka a aukuwar lamarin.
Gwamnatin Nijeriya ta bayar da wa’adin mako biyu don bincike kan mutuwar mutum 37 a hannun NSCDC
Olubunmi Tunji-Ojo, Ministan Harkokin Cikin Gida na Nijeriya / X/@MinOfInteriorNG

Ministan harkokin cikin gida na Nijeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayar da wa’adin mako biyu ga kwamitin mutum 10 mai zaman kansa da gwamnatin tarayyar ƙasar ta kafa don yin bincike kan mutuwar mutum 37 a hannun rundunar tsaro ta NSCDC a jihar Neja.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta Nijeriya ta wallafa a shafinta na X ranar Talata ta ambato ministan yana kira ga kwamitin ya yi aiki cikin ‘yanci ba tare da tsoma bakin kowa ba, yana mai jaddada cewa adalci shi ne abin da ya fi dacewa a yi wa mamatan da iyalansu.

Sanarwar ta ce an bai wa kwamitin aikin gano aihinin adadin mutanen da suka mutu da yanayin da ya haddasa mutuwarsu ta hanyar amfani da binciken kimiyya.

Kazalika aikin kwamitin ya haɗa da tabbatar da ko akwai sakaci da aikata ba daidai ba da haɗin baki ko keta doka a aukuwar lamarin.

Har wa yau gwamnatin Nijeriya tana buƙatar kwamitin ya ba da shawarwari game da matakan hukunci da suka dace da kuma diyyar da ta kamata a bai wa iyalan waɗanda suka mutu.

Masu AlakaTRT Afrika - An gudanar da zanga-zangar neman a kubutar da daruruwan mutane da aka yi garkuwa da su a jihar Neja

Haka kuma an buƙaci kwamitin ya bayar da shawara kan matakan da suka kamata a ɗauka domin hana sake aukuwar irin lamari.

Dakta Tunji-Ojo ya umarci shugabannin NSCDC da jami’an da lamarin ya shafa su ba da cikakken haɗin kai ga kwamitin kuma su kare dukkan bayanai da hujjoji da ke da alaƙa da lamarin, in ji sanarwar.

Ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na lalata ko kuma ɓoye hujja ko tsoratar da shaidu ko kuma yin ƙafar-ungulu ga binciken za a ɗauke shi ne a matsayin laifi mai muni.

 Za mu yi komai cikin gaskiya. Wannan kwamitin zai ba ku gaskiyar lamari. Babu wani hafsa, duk girman matsayinsa, da za a kare idan aka same shi da laifi,” kamar yadda sanarwar ta ambato shi yana bayyanawa ga ‘yan Nijeriya.

Kwamitin da ke ƙarƙashin jagorancin Mista Jonathan Kure, ana sa rai zai fara aiki ne nan-take kuma ya miƙa rahotonsa cikin makonni biyu.

Rumbun Labarai
'Yanbindiga sun kashe mutum tara a jihar Filaton Nijeriya
An kama mai PoS da ake zargi da aiki da taimakon mai garkuwa da mutane
An tsare kwamandan NSCDC da wasu jami'an hukumar na jihar Neja kan mutuwar masu haƙar ma'adinai 37
Gwamnatin Nijeriya ta kafa kwamitin mutum 10 don binciken mutuwar mutum 37 a hannun NSCDC a Neja
Waɗanda suka tsira a Jihar Neja sun bayyana yadda abokan sana'arsu suka rasu a ɗakin da aka tsare su
Ana zargin giya ta kashe mutum 49 a Jihar Ondo da ke kudancin Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da kwamandan NSCDC bisa mutuwar masu haƙar ma'adinai 37 a jihar Neja
Majalisar Wakilan Nijeriya ta aika da ƙudirin kafa ’yansandan jihohi ga majalisun dokokin jihohi
Rikicin Amurka da Iran: NLC ta nemi gwamnatin Nijeriya ta ɗauki mataki bayan litar mai ta kai N1,500
Dakarun Nijeriya sun kubutar da mutane 31 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Kebbi
Rundunar sojin Nijeriya 'ta kashe ‘yanta’addan Boko Haram da ISWAP fiye da 1000 a shekara ɗaya'
Samun ɗa namiji magaji ba ya gabana - Aliko Dangote
Rundunar 'yansandan Nijeriya ta yi gargaɗi game da yiwuwar kai hare-hare makarantu da wuraren ibada
Ana zargin ‘yanta’adda da kashe aƙalla mutum 13 a wasu hare-hare a Jihar Filato ta Nijeriya
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum 262, sun kuma ceto 27 da aka yi garkuwa da su
An sace malamai shida da suka je taron addu’ar APC a Zamfara
Gwamnatin Nijeriya ta yi Allah wadai da kisan 'yan ƙasarta biyu a Afirka ta Kudu
FBI ta nemi haɗin kan EFCC don gudanar da bincike kan zargin karkatar da kuɗaɗen tallafin Amurka
Majalisar Dokokin Nijeriya ta dakatar da ziyarar aiki zuwa Afirka ta Kudu
Tinubu ya bai wa kowace 'yar tawagar ƙwallon kwandon Nijeriya dala dubu ɗari-ɗari