| Hausa
TATTALIN ARZIKI
3 minti karatu
Zuba jari a ɓangaren makamashi na Nijeriya na iya ƙaruwa cikin shekaru biyar – Hukumar IEA
Babban Daraktan hukumar IEA Fatih Birol, Nijeriya na bukatar dimbin jarin kudi domin bunkasa damarmakin da take da su a bangarorin man fetur da iskar gas da makamashi da ake sabuntawa, musamman na hasken rana.
Zuba jari a ɓangaren makamashi na Nijeriya na iya ƙaruwa cikin shekaru biyar – Hukumar IEA
Zuba jari a bangaren makamashi na Nijeriya na iya ninkawa cikin shekaru biyar – Hukumar IEA

Nijeriya na iya ninka yawan jarin da ake zubawa a bangaren makamashinta cikin shekaru biyar masu zuwa, bayan da kasar ta zama mamba mai alaƙa da Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA), a cewar Babban Daraktan hukumar, Fatih Birol.

Birol ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai Abuja, inda ya ce sabuwar hadakar za ta taimaka wajen jawo karin hannayen jari da karfafa haɗin gwiwar fasaha da kuma bai wa Nijeriya damar taka muhimmiyar rawa a tattaunawar manufofin makamashi na duniya.

“Burina shi ne, cikin kankanin lokaci, wato shekaru biyar, a kalla a ninka jarin da ake zubawa Nijeriya a bangaren makamashi fiye da yadda ake samu a yanzu,” in ji Birol.

Ya ce Nijeriya na bukatar dimbin jarin kudi domin bunkasa damarmakin da take da su a bangarorin man fetur da iskar gas da makamashi da ake sabuntawa, musamman na hasken rana.

A cewar Birol, dimbin albarkatun makamashi da Nijeriya ke da su, da kuma sauye-sauyen da ke samu a harkokin cinikayyar makamashi a duniya, na iya sanya kasar ta zama wurin da gwamnatoci da masu zuba jari masu zaman kansu za su fi sha’awar saka jari.

“Mafi darajan albarkatun da ake da shi, ba man fetur ba ne ko iskar gas ko kuma uranium da lithium ba, amana ce. Kasashe na neman abokan hulda da za su iya yarda da su,” in ji shi.

Birol ya bayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da za a iya dogaro da ita wajen samar da makamashi, yana mai cewa fitar da kayayyakin man fetur daga matatar Dangote ya taimaka wajen rage matsin lambar karancin man fetur a Turai a 'yan watannin baya-bayan nan.

Matatar, wadda ke da karfin tace kusan ganga 700,000 na danyen mai a kowace rana, ta kara yawan kayayyakin man fetur da take fitarwa zuwa kasuwannin duniya.

A watan Yuli Nijeriya ta zama mamba da ke alaƙa da IEA, bayan ƙasashe mambobin hukumar, ciki har da Amurka da Jamus da Italiya da kuma Japan, sun amince da bukatar ƙasar baki daya.

Ana sa ran IEA da gwamnatin Nijeriya za su rattaba hannu kan wani shirin haɗin gwiwa a Abuja, wanda zai kunshi bangarorin iskar gas da samar da wutar lantarki da makamashi mai tsafta da inganta tattara bayanan makamashi.

Ana kuma sa ran haɗin gwiwar za ta taimaka wa Nijeriya wajen inganta tsarin tattara da bayar da bayanan makamashi, musamman kan hakar danyen mai, fitar da shi zuwa kasashen waje da kuma yawan man da ake amfani da shi a cikin gida.

Masu zuba jari da masu ruwa da tsaki a kasuwannin makamashi sun ɗaɗe suna kallon gibin da ke akwai wajen tattara bayanan makamashi a Nijeriya a matsayin wata babbar matsala.

Ƙazalika Nijeriya na burin kara yawan danyen man da take hakowa zuwa ganga miliyan uku a kowace rana nan da shekarar 2030, wanda ya kusan ninka adadin da take hakowa a yanzu.

Gwamnatin ƙasar na dogaro kan sauye-sauyen da ake yi a bangaren makamashi da inganta ababen more rayuwa da kuma karfafa tsaro domin rage satar mai da kuma jawo saka jari daga kasashen waje, bayan shekaru da dama na karancin zuba jari a bangaren.