| Hausa
TATTALIN ARZIKI
2 minti karatu
Hauhawar farashin kayayyaki a Ghana ta ƙaru a wata uku a jere da 5.3% a Yunin 2026
Hukumar ƙididdiga ta Ghana ta ce hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru a wata na uku a jere a watan Yuni, zuwa kashi 5.3 a shekara daga kashi 3.7 a watan Mayu.
Hauhawar farashin kayayyaki a Ghana ta ƙaru a wata uku a jere da 5.3% a Yunin 2026
Hukumar kididdiga ta ce hauhawar farashin kayayyaki a Ghana ta karu a wata na uku a jere a watan Yuni / TRT Afrika Hausa

Hukumar ƙididdiga ta Ghana, a ranar Laraba ta ce hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya ƙaru a wata na uku a jere zuwa watan Yuni, inda ta kai kashi 5.3 cikin 100 a cikin shekara ɗaya daga kashi 3.7 cikin 100 a watan Mayu.

Masanin ƙididdiga na gwamnati Alhassan Iddrisu ya danganta ƙaruwar farashin kan kayayyaki da ba na abinci ba, ciki har da sufuri, gidaje, da fannin ilimi.

Hauhawar farashin kayayyakin ta kasance ƙasa da kashi 13.7 cikin 100 a irin wannan wata a bara, in ji Iddrisu yana mai ƙari da cewa an ƙara samun matsi na farashin kayayaki.

Ƙasar da ta yi fice wajen samar da zinare da man fetur da koko, ta fara fita daga mummunan yanayin matsin tattalin arziki da ta faɗa a cikin shekaru da dama.

'Ta cancanci sa ido sosai'

"Ƙaruwar farashin kayayyaki da aka samu a kwanan nan ta cancanci sa ido sosai don tabbatar da nasarorin da aka samu a baya," kamar yadda Idrissu ya shaida wa manema labarai.

Kazalika Hukumar ƙididdiga ta Ghana ta ce kayayyakin da ake samarwa a cikin gida sun ba da gudunmawar fiye da kashi 86 cikin 100 ga ƙaruwar farashin kayayyaki.

Babban Bankin Ghana na shirin ɗaukar mataki kan darajar riba da ake samu a ƙarshen wannan watan.

Ya dakatar da shirin zagayen rage darajar kuɗi a watan Mayu saboda damuwa kan hauhawar farashin kayayyaki.

Rumbun Labarai
Kayan da Turkiyya ta fitar zuwa Afirka a 2026 sun haura na dala biliyan 13
Kuɗin Ghana ya koma fuskantar matsi, na Uganda na farfaɗowa, na Nijeriya zai iya sauyawa kaɗan
Amurka ta yi barazanar saka wa tattalin arzikin Iran takunkumin da 'duniya ba ta taɓa gani ba'
Gwamnatin Nijeriya za ta farfado da burtalan kiwo 417 a faɗin ƙasar
Za a gyara kamfanin NNPC tare da sayar da hannayen jarinsa a kasuwar hannayen jarin Nijeriya —Tinubu
Matatar Dangote ta fitar da tan fiye da 400,000 na man jiragen sama zuwa Turai a watan Yuli - Rahoto
Hukumar Kasuwanci Marar Shinge ta Afirka ta sanya hannu da wani kamfanin Nijeriya don inganta fito
A lokacin da cututtuka suka tsallaka iyaka: Manoman Afirka na neman sabbin matakan kariya
Farashin fetur a Amurka ya tashi sakamakon tsaiko a Hormuz da sanarwar Houthi ta rufe Bahar Maliya
ECOWAS ta sanya hannu kan yarjejeniyar tallafa wa aikin bututun iskar gas na Nijeriya da Morocco
Ƙungiyar EU ta sanar da sanya sabbin takunkumai kan cinikayyar zinare a Sudan
Wa yake amfana a lokacin da tattalin arzikin duniya ke ci da wuta sakamakon yaƙi?
Abubuwan da dalar Amurka Tiriliyan 1.1 mallakin Elon Musk za ta iya yi a Afirka
Elon Musk ya zama tiriloniya na farko a tarihin duniya
An zargi matatar mai mafi girma a Afirka da ƙoƙarin yin babakere game da man Nijeriya
Biliyoyin kudi da gangunan mai: Yadda matatar mai ta Dangote ke ƙarfafar Afirka da makamashi
China ta faɗaɗa janye haraji baki ɗaya ga kayan da ta shigar daga ƙasashen Afirka 53
Wasu daga waje na ƙoƙarin daƙile ci-gaban Afirka, in ji  Dangote
Ghana ta bai wa wani kamfanin ƙasar lasisin haƙar zinare kan $1bn
Shigar kuɗaɗe daga waje cikin Nijeriya don zuba jari ta ƙaru da kusan kashi 90% a 2025 – Hukumomi