Abubuwan da dalar Amurka Tiriliyan 1.1 mallakin Elon Musk za ta iya yi a Afirka
TATTALIN ARZIKI
4 minti karatu
Abubuwan da dalar Amurka Tiriliyan 1.1 mallakin Elon Musk za ta iya yi a AfirkaA ranar 12 ga Yunin 2026, Elon Musk - dan kasuwar Amurka da aka haifa a Afirka ta Kudu - ya zama mutumin da ya fi kowa kudi a duniya inda ya mallaki kudi a kalla dalar Amurka tiriliyan daya.
Elon Musk ne mutumin da ya fi kowa kudi a duniya da inda ya mallaki sama da dala tiriliyan 1,1 / Reuters

A ranar 12 ga Yunin 2026, Elon Musk - wani ɗan kasuwa ɗan asalin Afirka ta Kudu ɗan kasar Amurka - ya zama mutum na farko a duniya da ya mallaki kudi da suka kai akalla dalar Amurka tiriliyan 1.

Forbes da Bloomberg sun ba da rahoton a ranar Lahadi, 14 ga Yuni, cewa dukiyar Musk na da kudi sama da dalar Amurka tiriliyan 1.1.

Arzikin Musk ya ƙaru sosai bayan da hannun jarin kamfaninsa na SpaceX ya yi tashin gwauron zabi a lokacin fara hada-hada a kasuwar hannayen jari.

SpaceX kamfani ne na makaman roka, sadarwa, da Kirkirarriyar Basira, wanda darajarsa ta kai dala tiriliyan 2.2 a rana ta farko da ya shiga kasuwar hannayen jari ta Nasdaq da ke Amurka.

Kaso mai yawa sosai

Musk yana da kusan kashi 42% na jimillar hannun jarin kamfanin. Wannan ya ba shi iko sosai kan duk abin da yake yi.

Bayan an saka hannun jarin a wannan kamfani, hannun jarin SpaceX ya rufe wannan rana da dala $161 kowanne hannu a ranar 12 ga Yuni, inda ciniki na farko ya tara dala biliyan $75.

A cewar Bloomberg, hannun jarin Musk a SpaceX ya kai akalla dala biliyan $767.

A yanzu, ƙimar kamfanin ta dogara ne akan kyakkyawan fata game da yiwuwar kasuwancinsa. A halin yanzu, yana asarar kuɗi fiye da yadda yake samu.

Na iya daukar nauyin kashe-kashen kudaden manyan kasashen Afirka

Baya ga wannan, me dala tiriliyan 1 za ta iya yi a yanayin Afirka?

Na farko, ta hanyar amfani da kimanta kasafin kuɗi na manyan ƙasashe 20 na Afirka, dukiyar Musk za ta iya biyan dukkan buƙatun kasafin kuɗinta na tsawon shekara guda ba tare da rance ba, kuma su bar kusan dala biliyan 300 da ba a yi amfani da su ba.

Afirka ta Kudu, Aljeriya, Masar, Maroko, Angola, Najeriya, Kenya, Cote d'Ivoire, Tunisia, da Tanzania suna da kasafin kuɗi 10 mafi tsada a nahiyar a kowace shekara, tun daga dala biliyan 21 zuwa dala biliyan 128.

Binciken TRT Afrika kan manyan kasafin kuɗi 20 na nahiyar na shekarar 2025 ya nuna ya kai kusan dala biliyan 715.

Ilimi

Idan muka koma ga ilimi, don gabatar da hujjojin misali, za mu yi amfani da birnin Afirka mai mafi girman kuɗin ilmantar da yaro a ƙarƙashin manhajar karatu ta ƙasa da ƙasa - kuma wannan shi ne babban birnin Kenya, Nairobi, a cewar Bayanan Makarantun Ƙasa da Ƙasa.

A Nairobi, matsakaicin kuɗin makaranta a ƙasashen duniya yana kusa da dala 7,100 a kowace shekara. Wannan yana nufin cewa dukiyar Musk ta dala tiriliyan 1.1 za ta iya ɗaukar nauyin karatun kusan ɗalibai miliyan 155 na shekara guda.

A matsakaicin shekaru 12 a ilimin firamare, wanda bai haɗa da da karatun manyan makarantu ba, Musk zai iya ɗaukar nauyin kusan yara miliyan 13 a wata makarantar ƙasa da ƙasa a Nairobi.

Kuma game da kiwon lafiya, matsakaicin kuɗin kula da lafiya na shekara-shekara na kowane mutum a Afirka ta Kudu shi ne mafi yawa a Afirka.

Matatun mai na Dangote guda 55

A cewar Bankin Duniya, matsakaicin na’auni kowanne mutum a Afirka ta Kudu na kashe kusan dala 540 a don kiwon lafiya kowace shekara. Jimillar dukiyar Musk za ta iya kula da lafiyar mutane biliyan 2 - ko kuma daya bisa hudu na jama’ar duniya - a ƙarƙashin tsarin kiwon lafiya na Afirka ta Kudu na tsawon shekara guda.

Mafi girman matatar mai a Afirka ita ce matatar mai ta Dangote mai darajar dala biliyan 20 da ke Najeriya. Arzikin Musk zai iya gina irin wannan tatata har guda.

Kuma a ƙarshe, a wasanni, filin wasa mafi tsada a Afirka shi ne filin wasa na Cape Town na Afirka ta Kudu, wanda aka gina akan kuɗi har dala miliyan 600, kuma an kammala shi a shekarar 2009. Musk zai iya gina irin su har guda 1,833.

Bari mu ƙara gargaɗin cewa Musk ba shi da tsabar kuɗi na dala tiriliyan 1.1. Yawancin dukiyarsa tana da alaƙa da hannun jarin kamfani waɗanda dole ne a sayar don a mayar da su zuwa tsabar kuɗi.