| Hausa
TATTALIN ARZIKI
3 minti karatu
Amurka ta yi barazanar saka wa tattalin arzikin Iran takunkumin da 'duniya ba ta taɓa gani ba'
Takunkumin "zai haɗa abubuwa da dama," kamar yadda Bessent ya shaida wa gidan talbijin na Newsmax a ranar Alhamis, yana mai ƙari da cewa za a ci gaba da rufe Mashigar Hormuz da kuma hana komai shiga da fita daga tashoshin jiragen ruwan Iran.”
Amurka ta yi barazanar saka wa tattalin arzikin Iran takunkumin da 'duniya ba ta taɓa gani ba'
Sakataren Baitulmalin Amurka ya ce za a ci gaba da rufe Mashigar Hormuz tare da hana komai shiga da fita daga tashoshin jiragen ruwan Iran

Sakataren Baitulmalin Amurka Scott Bessent ya yi barazanar saka wa tattalin arziki Iran takunkumi wanda "duniya ba ta taɓa ganin irinsa ba" a mako mai zuwa.

Takunkumin "zai haɗa abubuwa da dama," kamar yadda Bessent ya shaida wa gidan talbijin na Newsmax a ranar Alhamis, yana mai ƙari da cewa za a ci gaba da rufe Mashigar Hormuz da kuma hana komai shiga da fita daga tashoshin jiragen ruwan Iran.”

"Ku ci gaba da sa ido kan wannan wuri don jin ƙarin sanarwa da za a fitar a mako mai zuwa," in ji shi.

Bessent ya bayyana wata hanya mai matakai biyu da ke nuna matsin lamba na kuɗi da kuma rufe tashoshin jiragen ruwan Iran.

A baya, Mataimakin Shugaban Ƙasar Amurka JD Vance ya ce babban abin da Amurka ta fi ba da fifiko a yaƙinta da Iran shi ne rage farashin mai ga Amurkawa, tare da hana Tehran sayen makaman nukiliya a matsayi na biyu.

Kalaman masu tsauri sun bambanta da wanda Bessent ya yi a ranar 4 ga Agusta, lokacin da ya shaida wa CNBC cewa za a iya cim ma yarjejeniya da Tehran don sake buɗe Mashigar Hormuz cikin 'yan kwanaki.

Waɗannan kalaman sun sanya hannayen-jarin Amurka sun yi tsada kana farashin mai ya ragu.

A watan Yuli, Ma'aikatar Baitulmalin ƙasar ta faɗaɗa takunkumin da ta ƙaƙaba wa kamfanonin jigilar kaya da na kuɗi na Iran bayan sabbin hare-haren da Iran ta kai wa jiragen ruwa na ƙasashen duniya a Mashigar Hormuz.

Yaƙin Amurka da Iran

Amurka ta haɗa kai da Isra'ila wajen kai wa Iran hari a ranar 28 ga watan Fabrairu, inda hare-haren suka kashe Shugaban Addinin musulunci na ƙasar wanda ya daɗe yana mulki, Ali Khamenei, da wasu manyan jami'an gwamnati da kuma ɗaruruwan fararen-hula

Iran ta mayar da martani cikin sauri ta hanyar riƙe iko da Mashigar Hormuz, muhimmiyar hanya da ake wuce wa da kashi ɗaya bisa biyar na man fetur na duniya, kuma ta yi ruwan makamai masu linzami da jiragen sama maras matuƙa a kan kasashen yankin Gulf da ke ƙawance da Amurka, wanda hakan ya gurgunta harkokin tattalin arziki na ƙasashen masu arzikin mai.

Rundunar sojojin Amurka ta rawaito cewa an lalata mata tarin makamai masu linzami masu matukar tsada da sauran makamai a cikin watanni da ake yaƙin waɗanda kuɗaɗen sun haura biliyoyin daloli, kana wasu rahotannin sun yi nuni da cewa ana samu raguwa na makaman sosai, lamarin da ke taƙaita zaɓin Shugaban Amurka Donald Trump na sake kai hare-hare kan Iran.

"Wasu lokutan muna mai da hankali kan ɓangaren makamashi saboda muna son Amurkawa su samu farashi mai rahusa na mai da iskar gas. Wasu lokutan kuma muna mai da hankali kan sojoji... kan shirin nukiliya," in ji Vance.

A kwanan nan, Trump ya ce zai daina kai wa Iran hari ne kawai idan aka cim ma yarjejeniyar sake buɗe Mashigar Hormuz cikin sauri.

Yanzu Iran ta tsara wasu jerin sharuɗɗa don sake buɗe hanyar wanda ake ganin gwamnatin Trump ba za ta amince da ita ba: kamar kawo karshen yaƙin a dukkan fannoni da dage shingayen Amurka a tashoshin jiragen ruwa na Iran da kawo ƙarshen takunkumai da Amurka ta ƙaƙaba da sakin kadarorin da ta hana amfani da su da kuma biyan diyya ga ɓarnar da aka yi a lokacin yaƙin.

Waɗannan sharuɗɗan sun yi daidai da yarjejeniyar fahimtar juna wacce aka cim ma a watan Yuni kuma ta ruguje yayin da rikici ya sake kaurewa.

Kazalika yarjejeniyar ta haɗa har da tanadin ƙirƙirar asusun sake gina Iran na dala biliyan 300.

Rumbun Labarai
Matatar Dangote ta sayar da hannayen-jarin fiye da naira biliyan 10 mintuna kaɗan bayan ƙaddamarwa
Matatar Dangote za ta buɗe sayar da hannayen-jari na Naira tiriliyan 2.15
Apple ya gabatar da iPhone Duo, wayarsa ta farko da ake rufewa
Aliko Dangote ya ƙaddamar da fara sayar da hannun-jarin matatar mansa ga jama'a
Uganda ta sanar da samun raguwar kaso 15% a hada-hadar fitar da kofi zuwa ƙasashen waje
Zuba jari a ɓangaren makamashi na Nijeriya na iya ƙaruwa cikin shekaru biyar – Hukumar IEA
Matatar Dangote ta Nijeriya za ta fara sayar da hannayen jari a karon farko nan da ‘yan kwanaki
Shirin bankin da ba ya karɓar ruwa ba don tallata wani addini ba ne – Gwamnan Babban Bankin Ghana
Trump ya soki Canada kan haraji cikin rigimar cinikayyar da Amurka ke yi da ƙasar
Kayan da Turkiyya ta fitar zuwa Afirka a 2026 sun haura na dala biliyan 13
Kuɗin Ghana ya koma fuskantar matsi, na Uganda na farfaɗowa, na Nijeriya zai iya sauyawa kaɗan
Gwamnatin Nijeriya za ta farfado da burtalan kiwo 417 a faɗin ƙasar
Za a gyara kamfanin NNPC tare da sayar da hannayen jarinsa a kasuwar hannayen jarin Nijeriya —Tinubu
Matatar Dangote ta fitar da tan fiye da 400,000 na man jiragen sama zuwa Turai a watan Yuli - Rahoto
Hukumar Kasuwanci Marar Shinge ta Afirka ta sanya hannu da wani kamfanin Nijeriya don inganta fito
A lokacin da cututtuka suka tsallaka iyaka: Manoman Afirka na neman sabbin matakan kariya
Farashin fetur a Amurka ya tashi sakamakon tsaiko a Hormuz da sanarwar Houthi ta rufe Bahar Maliya
ECOWAS ta sanya hannu kan yarjejeniyar tallafa wa aikin bututun iskar gas na Nijeriya da Morocco
Ƙungiyar EU ta sanar da sanya sabbin takunkumai kan cinikayyar zinare a Sudan
Hauhawar farashin kayayyaki a Ghana ta ƙaru a wata uku a jere da 5.3% a Yunin 2026