| Hausa
TATTALIN ARZIKI
2 minti karatu
Shirin bankin da ba ya karɓar ruwa ba don tallata wani addini ba ne – Gwamnan Babban Bankin Ghana
Babu wani addini da aka dora wa alhakin kula da ayyukan Bankin, kuma babu wani sabon mataki daga wani addini da aka shigar a tsarin gudanarwar bankin, in ji Dr Johnson Pandit Asiama.
Shirin bankin da ba ya karɓar ruwa ba don tallata wani addini ba ne – Gwamnan Babban Bankin Ghana
Babban Bakin Ghana

Gwamnan Babban Bankin Ghana (BoG), Dr Johnson Pandit Asiama ya tabbatar wa 'yan kasar, musamman al'ummar Kirista, cewa tsarin banki da ba ya karɓar ruwa da Ghana ke shirin aiwatarwa ba wata hanya ba ce ta inganta ko yada wani addini a kasar ba.

Dr Asiama ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin wata ganawa da shugabannin addinai a Accra, inda ya yi ƙarin bayani kan tsarin dokoki da ka'idojin da za su jagoranci gudanar da bankin da ba ya karɓar ruwa.

Kazalika ya ce tsarin wani nau'in harkar kuɗi ne na kasuwanci wanda kowa zai iya amfana da shi ba tare da la'akari da addininsa ba.

"Babu wani addini da aka dora wa alhakin kula da ayyukan bankin, kuma babu wani sabon mataki daga wani addini da aka shigar a tsarin gudanarwar bankin,’’ in ji Asiama, yana mai kari da cewa bankin zai inganta tsarin hada-hadar kuɗi bisa ka'idojin ɗoka ta shekarar 2016 wato ‘‘Banks and Specialised Deposit Taking Institutions Act.’’

"Aikinmu kawai shi ne samar da tsarin dokoki da kulawa da cibiyoyin da ke da lasisi za su iya gudanar da wannan tsarin banki na kasuwanci wanda ya bai wa kowa da kowa dama ba tare da nuna bambanci ba.’’

Rumbun Labarai
Kotun Kenya ta ce a dakatar da aikin Matatar Mai ta Dangote ta dala biliyan 16
Dangote na shirin zuba jarin $10bn don shawo kan matsalar wutar lantarki a Nijeriya
Amurka ta ƙulla yarjejeniyar $414m kan aikin haƙar uranium a Nijar
Matatar Dangote ta sayar da hannayen-jarin fiye da naira biliyan 10 mintuna kaɗan bayan ƙaddamarwa
Matatar Dangote za ta buɗe sayar da hannayen-jari na Naira tiriliyan 2.15
Apple ya gabatar da iPhone Duo, wayarsa ta farko da ake rufewa
Aliko Dangote ya ƙaddamar da fara sayar da hannun-jarin matatar mansa ga jama'a
Uganda ta sanar da samun raguwar kaso 15% a hada-hadar fitar da kofi zuwa ƙasashen waje
Zuba jari a ɓangaren makamashi na Nijeriya na iya ƙaruwa cikin shekaru biyar – Hukumar IEA
Matatar Dangote ta Nijeriya za ta fara sayar da hannayen jari a karon farko nan da ‘yan kwanaki
Trump ya soki Canada kan haraji cikin rigimar cinikayyar da Amurka ke yi da ƙasar
Kayan da Turkiyya ta fitar zuwa Afirka a 2026 sun haura na dala biliyan 13
Kuɗin Ghana ya koma fuskantar matsi, na Uganda na farfaɗowa, na Nijeriya zai iya sauyawa kaɗan
Amurka ta yi barazanar saka wa tattalin arzikin Iran takunkumin da 'duniya ba ta taɓa gani ba'
Gwamnatin Nijeriya za ta farfado da burtalan kiwo 417 a faɗin ƙasar
Za a gyara kamfanin NNPC tare da sayar da hannayen jarinsa a kasuwar hannayen jarin Nijeriya —Tinubu
Matatar Dangote ta fitar da tan fiye da 400,000 na man jiragen sama zuwa Turai a watan Yuli - Rahoto
Hukumar Kasuwanci Marar Shinge ta Afirka ta sanya hannu da wani kamfanin Nijeriya don inganta fito
A lokacin da cututtuka suka tsallaka iyaka: Manoman Afirka na neman sabbin matakan kariya
Farashin fetur a Amurka ya tashi sakamakon tsaiko a Hormuz da sanarwar Houthi ta rufe Bahar Maliya