| Hausa
TATTALIN ARZIKI
2 minti karatu
Hukumar Kasuwanci Marar Shinge ta Afirka ta sanya hannu da wani kamfanin Nijeriya don inganta fito
Sakatariyar Kasuwancin Afirka Marar Shinge ta kulla yarjejeniyar shekaru 20 kan tsabar kuɗi dala biliyan 3.1 da kamfanin 'Bergmans Security Consultants and Supplies Ltd' da ke Nijeriya don samar da tsarin fito na nahiyar baki ɗaya.
Hukumar Kasuwanci Marar Shinge ta Afirka ta sanya hannu da wani kamfanin Nijeriya don inganta fito
Sakatare Janar na AfCFTA Wamkele Mene ya ce tsarin fito da ba na zamani ba na dabbaka cin hanci, rage kudaden shiga ko kara wa.

Sakatariyar Yankin Kasuwanci Marar Shinge ta Afirka ta sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru 20, kan dala biliyan 3.1 tare da Bergmans Security Consultants and Supplies Ltd na Najeriya, don ƙaddamar da tsarin fito a duk faɗin nahiyar don haɓaka cinikin cikin Afirka da kuma rage kwararar kudaden shiga a cikin ƙasashe 50 mambobin kawancen.

Yarjejeniyar, wacce aka sanya hannu a Abuja a daren Laraba, za ta ba Bergmans kuɗi tare da kawo aikin sabunta ayyukan fito na AfCFTA don daidaita hanyoyin shiga da fitar da kayayyaki, da daidaita hanyoyin ƙetare iyaka da kuma samar da bin diddigin kayayyaki a ainihin lokaci a faɗin nahiyar.

Sakataren Janar na AfCFTA Wamkele Mene ya ce tsarin yin fito wanda ba na zamani ba yana bayar da gudunmawa wajen cin hanci da rashawa, da bacewar kudaden shiga, da ƙarancin lissafin kuɗi da kuma wuce gona da iri.

Mene ya ce ƙasashe 50 na Tarayyar Afirka sun amince da yarjejeniyar AfCFTA kuma ciniki a nahiyar Afirka ya karu zuwa dala biliyan 220 a shekarar 2024, wanda ya karu da kashi 12.5% ​​a shekara guda.

Ninka kasuwanci tsakanin ƙasashen Afirka

An tsara aikin sabunta ayyukan na fiton ne don tallafawa burin AfCFTA na ninka ciniki tsakanin ƙasashen Afirka nan da shekarar 2035 ta bin hanyoyin da suka dace, da tattara bayanai da kuma bin diddigin kaya a ainihin lokaci.

Bergmans ya ce zai aiwatar da aikin ta hanyar reshensa na AfriTrade CMP Ltd, tare da amfani da gogewa daga aikin sabunta fito na Najeriya, wanda Mene ya ce ya taimaka wajen haɓaka kuɗaɗen shigar hukumar hana fasa-ƙwauri ta ƙasar da kashi 90.4%.