Gwamnatin Amurka ta kulla yarjejeniyar aikin hakar Uranium din Nijar wadda ta kai dala miliyan 414, matakin da ke nuna wata sabuwar mu'amalar kasuwanci tsakanin Washington da Niamey, shekaru biyu bayan janye dakarun Amurka daga ƙasar.
Hukumar ‘US International Development Finance Corporation (DFC)’ ta Amurka ce ta amince da biyan kudin hakar uranium na Dasa, wanda kamfanin hakar ma'adinai na Kanada, Global Atomic zai gudanar da aikin.
Kamfanin ya bayyana Dasa a matsayin daya daga cikin wuraren da ke da ma’adanin uranium mai inganci a Afirka.
Ana sa ran aikin zai kara wa Amurka damar samun uranium, wani ma'adini da Washington ke dauka a matsayin mai matukar muhimmanci a bangaren makamashi da fannin nukiliyarta.
Global Atomic ya ce kamfanin ne yake da kashi 80 cikin 100 na aikin Dasa, yayin da gwamnatin Nijar ke da sauran kashi 20 cikin 100.
Matakin ya zo ne a daidai lokacin da Washington da Niamey ke ci gaba da fuskantar tsamin dangantaka tun bayan juyin mulkin soja da aka yi a Nijar a shekarar 2023.
A shekarar 2024 ne sabuwar gwamnatin mulkin Soji na ƙasar ta umarci dakarun Amurka da su fice daga Nijar, sannan ta kara karfafa alakar tsaro da Rasha.
Wasu shaidu kan lamarin sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa, jami'an Amurka sun lura da aikin Dasa a matsayin wata dama ta farfado da alakar tattalin arziki da Nijar tare da tabbatar da samun wani muhimmin ma'adini mai amfani ga harkokin makamashi.
Kalubalen tsaro da sufuri
Sai dai duk wannan ci gaban da aka samu, akwai kalubale na tsaro da sufuri da ke barazana ga aikin, la’akari da yadda Nijar ke fama da hare-haren ƙungiyoyin masu dauke da makamai.
Bisa wadannan dalilai, kafar Reuters ta ce Global Atomic ya soma nazari kan wasu hanyoyin fitar da uranium daga Nijar, ciki har da yiwuwar amfani da wata hanya da za ta bi ta Aljeriya kana ta ratsa hamadar Sahara, kamar yadda Reuters ta ruwaito.
Wurin harkar ma’adanin na Dasa yana yankin Agadez, kimanin kilomita 105 daga kudancin garin Arlit, daya daga cikin muhimman yankunan hakar uranium a Nijar.
Kazalika Global Atomic ya ce ana ci gaba da aiki da kuma shirye-shiryen gina masana'antar sarrafa uranium.
Haka kuma zuba jarin na Amurka ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takaddama tsakanin gwamnatin Nijar da kamfanin hakar ma'adinai na Faransa, Orano, wanda gwamnatin Nijar ta kwace iko da wasu kadarorinsa na uranium.
Tuni dai Orano ya soma shari'ar neman sasanci a rikicin ta hanyar kotun shiga tsakani ta kasa da kasa.
Nijar na daga cikin manyan kasashen da ke samar da uranium a duniya, yayin da muhimmancin ma'adinin ke karuwa a duniya duba da kokarin kasashe na tabbatar da samun isasshen makamashin da ake amfani da shi wajen samar da nukiliya da sauran bukatu na makamashi.

















