Uganda ta samu raguwar kaso 15.1 cikin 100 na fitar da albarkatun kofi a watan Yuli idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, a cewar bayanai daga Ma'aikatar Noma, a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalar fari mai tsanani wanda ya shafi harkokin noma a sassan kasar.
Ƙasar da ke yankin Gabashin Afirka, wacce ita ce babbar mai fitar da kofi a Afirka, a bara ta fitar da buhu 997,105 da suka kai nauyin kilogiram 60 a watan Yuli, adadin da ya ragu zuwa buhu 846,376 a bana.
Ko da yake Ma'aikatar ba ta ba wasu dalilai game da raguwar ba, sai dai ana zargin matsalar fari na tsawo lokaci da zama sanadi na lalata albarkatun gonaki da dama a sassan Uganda a cikin 'yan watannin nan, lamarin da ke barazana ga yawan amfanin gona.
Kofi da zinari na daga cikin manyan albarkatu da kasar Uganda ke fitarwa kuma sun zama manyan kayayyakin musayar kuɗi na ƙasashen waje.
Faduwar watan Yuli
A bangaren daraja kuwa, Uganda ta samu dala miliyan 204.1 daga fitar da kofi a watan Yulin bana, ƙasa da kashi 18.6% idan aka kwatanta da dala miliyan 250.7 da aka samu a bara.
Raguwar da aka samu a watan Yuli ta zo ne bayan da Uganda ta ba da rahoton albarkatun kofi da aka fitar a farkon shekarar.
A watan Maris, an samu karuwar fitar da kofi da kashi 2.9 cikin 100 da buhu 671,152 a rahoton shekara zuwa shekara da ake fitarwa.
Fitar da kofi ya zama muhimmin bangare na samun kudin ketare ga Uganda. A cikin watanni 12 zuwa Maris, kasar ta samu dala biliyan 2.4 daga fitar da kofi, wanda ya karu daga dala biliyan 1.8 a cikin watanni 12 da suka gabata, a cewar ma'aikatar noma.
Uganda ita ce babbar mai fitar da kofi a Afirka, sai Habasha da ke biye da ita, inda albarkatun ke taka muhimmiyar rawa a fannin kudaden shigar da kasar ke samu daga kayayyakin da ta ke fitarwa.

















