| Hausa
TATTALIN ARZIKI
3 minti karatu
Kotun Kenya ta ce a dakatar da aikin Matatar Mai ta Dangote ta dala biliyan 16
Kafar watsa labaran kasar Kenya ta Citizen Digital ta rawaito cewa, mutane 133 da suka shigar da karar sun kai karar ofishin Shugaban kasar Kenya William Ruto, da hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki, da kuma kamfanin Dangote.
Kotun Kenya ta ce a dakatar da aikin Matatar Mai ta Dangote ta dala biliyan 16
FILE PHOTO: Dangote ya ce yana hasashen matatar mai ta Lamu za ta lashe kudi dala biliyan 15 zuwa 16 da za a kammala nan da 2030.

Attajirin Afirka mafi kudi, Aliko Dangote, na fuskantar sabon kalubale yayin da yake shirin kaddamar da aikin gina matatar man fetur a yankin Gabashin Afirka.

An tsara gudanar da bikin fara aikin a ranar Laraba, 30 ga watan Satumba, sai dai wata kotu ta bayar da umarnin dakatar da aikin.

Wannan na zuwa ne bayan da wasu mazauna yankin Chandavai, wanda ke cikin gundumar Lamu inda ake shirin gina matatar man, suka shigar da kara a kotu domin kalubalantar shirin.

Kafar watsa labaran kasar Kenya ta Citizen Digital ta rawaito cewa, mutane 133 da suka shigar da karar sun kai karar ofishin Shugaban kasar Kenya William Ruto, da hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki, da kuma kamfanin Dangote.

‘Ba a dakatar da kaddamarwar ba’

Sai dai, Rukunin Kamfanonin Dangote ya bayyana cewa hukuncin da kotu ta yanke game da takaddamar mallakar fili ba zai dakatar da fara aikin gina matatar man fetur mai karfin tace ganga 700,000 a kowace rana a yankin Lamu ba.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa, umarnin da Kotun Kula da Muhalli da Filaye ta Malindi ta bayar ya bukaci a ci gaba da barin yanayin filin yadda yake a halin yanzu har sai an gudanar da zaman sauraron karar a ranar 14 ga watan Oktoba.

An bayar da umarnin kotun ne a ranar 25 ga watan Satumba, amma sai a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba, aka bayyana shi ga jama'a.

Kamfanin Dangote, wanda hamshakin attajirin Afirka Aliko Dangote ke da shi, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa kotun "ba ta dakatar da bikin kaddamar da aikin gina matatar man ba a wannan matakin."

Duk da haka, kamfanin ya amince cewa hukuncin na iya shafar ayyukan da ake gudanarwa a wurin, kasancewar an bukaci bangarorin biyu su daina gudanar da duk wani aiki har sai an saurari karar.

Koyi da Matatar Dangote

Matatar mai ta Lamu da ke gabar tekun Kenya na da nufin yin koyi da nasarar da matatar Dangote ke samu na ganga 700,000 a kowace rana kusa da babban birnin kasuwancin Najeriya, Legas.

Amma ba kamar Najeriya ba, babbar mai samar da mai a yankin kudu da hamadar Sahara, Kenya a halin yanzu ba ta da man fetur mai yawan da za a iya kasuwancin sa.

Duk da haka, shugaban Kenya William Ruto ya ce matatar za ta samo danyen mai daga ko'ina cikin kasashen Gabashin Afirka, ciki har da Uganda, Sudan ta Kudu da Kenyan kanta.

Dangote ya ce yana sa ran matatar mai ta Lamu za ta lashe dala biliyan 15 zuwa dala biliyan 16 kuma yana fatan kammala ta nan da shekarar 2030.

Babban burin shi ne a saukaka samar da mai ga Gabashin Afirka, wacce a halin yanzu ke shigo da dukkan kayayyakin man fetur dinta duk da cewa yankin na da albarkatun danyen mai.

Haka nan yana cikin shirin Dangote na taimakawa wajen tabbatar da "dogaro da kai" ga makamashin Afirka.