Sojojin Yemen sun ce sun kama wasu mambobin tawagar Houthi da ke sarrafa jiragen yaƙi marasa matuƙa a lardin Taiz, yayin da gwamnan lardin ya yi gargaɗin cewa toshe hanyoyin shigar da man fetur da Houthi ke yi ya tilasta dakatar da wasu muhimman ayyuka a birnin.
Birged ta 35 mai sulke ta sojojin Yemen ta bayyana a cikin wata sanarwa ranar Jumma’a cewa dakarunta sun kama tawagar ne a yankin fagen daga na Al-Aqrud-Kahlan, da ke kudu maso gabashin Taiz.
Birged ɗin ta ce aikin na daga cikin ƙoƙarin dakile ayyukan Houthi da ƙarfafa shirin yaƙi a layukan gaba. Sai dai ba ta bayyana adadin mutanen da aka kama ba ko kuma cikakken bayani kan yadda aka gudanar da aikin.
Har yanzu Houthi ba ta mayar da martani kan sanarwar sojojin ba.
Kamen ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara tsananta faɗa a lardin kudu maso yammacin ƙasar, inda rikici da takaita hanyoyin samar da kayayyaki suka ƙara ta’azzara matsalolin jin kai tare da raba dubban mutane da muhallansu.
An dakatar da muhimman ayyuka
A nasa ɓangaren, Gwamnan Taiz, Nabil Shamsan ya ce tashoshin samar da wutar lantarki da ruwan sha, da kuma ayyukan kwashe shara a birnin, sun daina aiki saboda Houthi ta hana shigar da man fetur.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a Facebook, Shamsan ya ce, “Houthi ta kewaye Taiz tare da rufe dukkan hanyoyin shiga birnin tsawon kwanaki 15 da suka gabata.”
Ya ƙara da cewa asibitoci ma sun kasa bayar da cikakkiyar kulawar lafiya saboda ƙarancin magunguna da kayan aikin jinya.
Shamsan ya yi gargaɗin cewa yanayin rayuwa zai iya ƙara taɓarɓarewa ga kusan mutane miliyan huɗu da suka rasa matsugunansu da sauran mazauna Taiz, yayin da ƙungiyoyin agaji ke fuskantar matsalar isa gare su.
Farmakin ‘Dawn of Yemen’
A ranar 5 ga Oktoba, dakarun gwamnati sun ƙaddamar da wani farmaki mai suna “Dawn of Yemen” — wato Wayewar Yemen.
Shugaban Majalisar Shugabancin Yemen, Rashad al-Alimi, ya ce manufar farmakin ita ce dawo da cibiyoyin gwamnati da Houthi ke iko da su da kuma sake ƙwato babban birnin ƙasar, Sanaa.
A ranar 11 ga Oktoba, sojojin sun ce sun sake ƙwato wasu tuddai biyu a yankin Al-Aqrud, da ke kudancin Taiz.
A ranar 6 ga Oktoba ma, sojojin sun ce sun kashe mayaƙan Houthi 100 tare da kakkabo jiragen yaƙi marasa matuƙa guda biyar yayin ayyukan soji a wasu sassan lardin, ciki har da Al-Aqrud.
Yemen na cikin rikici tun shekarar 2014, lokacin da Houthi ta ƙwace babban birnin Sanaa da wasu larduna.
A watan Maris na 2015, wani kawancen ƙasashe ƙarƙashin jagorancin Saudiyya ya shiga yaƙin domin tallafa wa gwamnatin Yemen da ƙasashen duniya suka amince da ita.
Sabon tsananta rikicin, wanda ya fara a watan Yuli, ya haifar da faɗa mafi girma tun bayan tsagaita wutar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta taimaka wajen cimmawa a shekarar 2022, wadda ta kawo ɗan sauƙi a fadan.






















