| Hausa
KASUWANCI
3 minti karatu
Wasu daga waje na ƙoƙarin daƙile ci-gaban Afirka, in ji Dangote
“Ba za ka iya samun kasuwa ɗaya tilo ba . Kuma ka san , dole ka kuma tuna cewa akwai muradu na ƙasa da ƙasa , a gafar ce ni kan abin da nake faɗa, wannan muradin na ƙasashen waje ba ya son ta ga Afirka ta ci gaba .”
Wasu daga waje na ƙoƙarin daƙile ci-gaban Afirka, in ji  Dangote
Aliko Dangote, babban attajirin Afirka / AA
17 Afrilu 2026

Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya ce muradun wasu daga waje suna aiki domin hana Afirka ci-gaba.

Babban attajirin ya faɗi wannan ne ranar Alhamis a wani taro kan zuba jari a Afirka da aka yi a gefe yayin tarukan da ake na lokacin bazara na asusun ba da lamuni na IMF da bankin duniya a birnin Washington, DC.

Yayin da yake kira da a ƙara ƙarfafa haɗin kai a yanki, attajirin mai ba da kyauta ya yi watsi da yiwuwar ƙaddamar da kasuwa ta bai ɗaya a Afirka ba tare da kasuwannin yanki masu aiki ba .

“Tsarin kasuwanci tsakanin ƙasashen Afirka ba tare da shamaƙi ba zai yi aiki, amman zai iya aiki ne kawai lokacin da kasuwannin yankuna suka fara aiki,” in ji mai masana’antun.

Dangote ya ce dole kasuwannin yankuna su yi aiki tukun kafin a fara magana game da kasuwa ta baiɗaya ta Afirka.

“Ba za ka iya samun kasuwa ɗaya tilo ba . Kuma ka san , dole ka kuma tuna cewa akwai muradu na ƙasa da ƙasa , a gafar ce ni kan abin da nake faɗa, wannan muradin na ƙasashen waje ba ya son ta ga Afirka ta ci gaba .”

Dangote ya ce Afirka ba ta sami ko wace matatar mai ba cikin shekaru masu yawa, yana mai cewa “akwai muradu [na wasu mutane] da yawa da ba sa ƙyale ” ayyukan gina matatu a sauran ƙasashe su faru.

Game da janyo jari daga ƙetare zuwa cikin nahiyar, ɗankasuwan ya jaddada cewa zuba jari daga ƙetare yana yawan dogara ne kan yadda ake ganin yiwuwar aukuwar hatsari.

Ya ce dole ‘yan Afirka su zuba jari a nahiyarsu kafin masu zuba jari daga ƙetare za su shigo.

“‘Yan ƙetare za su zuba jari. Amma ‘yan ƙetaren ma mutane ne masu wayo. Duk abin da ka faɗa game da hatsari, suna son su duba shi sau 10. Ta yaya za mu iya cire hatsarinsa ? Hanya ɗaya tilo da za mu iya kawar da hatsarin shi ne mu ‘yan Afirka mu yi gaba-gaba kuma mu nuna cewa hatsarin abin hatsari ne na kallo [kuma] ba asalin hatsari ba ne,” in ji Dangote.

“Idan ba na zuba jari a Afirka, babu yadda za ni je na gamsar da kowa daga wajen nahiyar ya zo ya zuba jari. Saboda haka, dole na nuna cewa hatsarin na yanayin kallo ne kawai.”

Attajirin ya ce babu wata ƙasa da ba ta da hatsari, “amma dole ka san yadda za ka rage wannan hatsarin ”.

Dangote ya yi kira ga ‘yan Afirka su zuba dukiyarsu a matsayin jari a yankin kuma maimakon saka su cikin asusun bankuna na ƙetare.

“A wasu lokuta ina bayyana cewa idan ana maganar zunzurutun takardar kuɗi ne, za a iya samun wasu mutane da suka fi ni takardar kuɗi, amma kada [ku] ajiye wannan kuɗin a wani bankin ƙetare. [Ku] dawo da su gida, ku zuba jari, wurin na da kyau, za ku samu kuɗi da yawa,” in ji shi.

“Amma muna da wannan matsalar ta neman masu zuba jari daga ƙetare ko da yaushe . Masu zuba jari daga ƙetare ba za su taɓa zuwa ba saboda masu zuba jari daga ƙetare sun fi mu wayo, saboda haka ba za su zo ba.”

Ya ce za su zo ne kawai a lokacin da suka ga cewa ‘yan Afirka sun jajirce, suna yi da gaske kuma “muna zuba jari da kuɗadenmu”.