Dakarun Operation Hadin kai da ke yaƙi da ta’addanci a arewa maso gabashin Nijeriya sun ayyana yin gagarumar nasara bayan wani babban jami’in da ke kula da harkokin kuɗin ƙungiyar ‘yanta’adda ta ISWAP ya miƙa wuya.
Wata sanarwa da muƙaddashin jami’in watsa labaran dakarun Operation Hadin kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar ranar Asabar ta ce mutumin ya yi saranda ne da misalin ƙarfe 6:45 na safe na ranar Asabar 25 ga watan Yuli a yankin Ladari–Jegarawa–Tunokalia da ke kan hanyar Gamboru zuwa Wulgo.
Sanarwar ta ƙara da cewa ɗanta’addan ya miƙa wuya ne tare da yara maza biyu, tana mai ƙarawa da cewa lamarin ya faru ne sakamakon hare-haren sama da na ƙasa da rundunar sojin ƙasar ke kai wa mafakar ‘yanta’addan.
“Bayanan farko sun nuna cewa ɗanta’addan ya yi aiki ne a matsayin babban jami’in da ke kula da kuɗi na ISWAP a Jubillaram, inda ya kasance mai kula da harkokin kuɗi da sufurin ƙungiyar,” in ji sanarwar.

“Ya miƙa wuya tare da yara maza biyu. Ababen da aka karɓa daga hannun ɗanta’addan sun haɗa da bindigar AK-47 ɗaya da gidajen harsasai huɗu da harsasai 101 masu girman milimita 7.62 da babur ɗaya da kuma kuɗi ₦40,000,” in ji ta.
Kazalika rundunar sojin ta ce ana kan yi wa mutumin tambayoyi domin samun bayanai da za su taimaka wajen ayyukan da sojin ƙasar ke yi na kai samame kan sauran wuraren da ‘yanta’adda suke a yankin.
“Miƙa wuyar irin wannan muhimmin jami’in kula da kuɗin alama ce ta gagarumar koma baya ga ISWAP, wadda ke nuna ƙarin taɓarɓarewar lamuran ƙungiyar da ikonta da kuma ɗorewarta a ƙarƙashin matsi babu ƙaƙƙautawa na Operation Hadin Kai,” in ji sanarwar.
Rundunar ta yi kira ga sauran ‘yanta’addan su yi amfani da damar da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bayar na miƙa wuya kafin ta damar ta wuce


















