| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Amurka ta tura rukunin farko na ’yan ci-rani zuwa Laberiya
Laberiya ta bayyana cewa za ta karɓi ’yan ƙasashen waje har mutum  1,200 da aka kora daga Amurka a cikin shekara guda.
Amurka ta tura rukunin farko na ’yan ci-rani zuwa Laberiya
An ga ma'aikatan hukumar Dawo da Mutane da Sake Tsugunar da su ta Laberiya suna kula da sabbin dawowan.

’Yan ci-rani 20 da aka kora daga Amurka sun isa Laberiya a ranar Alhamis, kasancewarsu rukunin farko daga cikin mutane har 1,200 da wannan ƙasa ta yammacin Afirka ta amince za ta karɓa.

Laberiya ita ce ƙasa ta baya bayan nan a Afirka da ta amince da karɓar ’yan ci-ranin da aka koro a ƙarƙashin tsauraran matakan shige da fice na Shugaban Amurka Donald Trump da ake muhawara a kai.

Wani jirgin sama da ya taho da mutane 20 ɗin ya sauka a filin jirgin saman ƙasar da ke ƙasa da ƙasa gabannin karfe 1:00 na rana agogon gida (1300 GMT), kamar yadda Kamfanin Labarai na AFP ya ruwaito.

Sun shiga wata motar bus, wadda sannan ta fice daga filin jirgin saman da ke kusa da babban birnin ƙasar, Monrovia.

An hango ma’aikatan Hukumar Mayar da ’Yan Gudun Hijira da Sake Tsugunar da Su ta Laberiya suna kula da sababbin baki da suka isan.


An hana ’yanjarida damar magana da ’yanci-rani

An hana ’yanjarida zuwa kusa kuma an ki ba su samu damar yin magana da bakin.

Laberiya ta sanar a ranar Talata cewa za ta karɓi ’yan ƙasashen waje har 1,200 da aka koro daga Amurka a cikin shekara guda.

Ta ce suna da “yancin fita daga ƙasar a duk lokacin da suke so” ko kuma su nemi mafaka (Asylum).

Gwamnatin ta ce “ba ta buƙaci ko ta karɓi wani diyya ko alƙawarin lada a matsayin sakamakon amincewarta na shiga cikin wannan shiri ba.”

Gwamnatin, wadda ta bayyana shirin a matsayin “na jin-ƙai gaba ɗaya,” ta ce “Laberiya za ta samu tallafi domin taimakawa wajen gudanar da wannan shiri da kuma ƙarfafa tsarin shige da fice gaba ɗaya” a matsayin ɓangare na wannan haɗin gwiwa.