Ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya sha alwashin mayar da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a shekarar 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da ‘yan jarida a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce zai tilasta wa duk wanda ya sace kuɗaɗen da aka ware domin tallafin man fetur mayar da su idan ya hau mulki.
Shugaba Bola Tinubu ne ya sanar da cire tallafin man fetur a ranar da aka rantsar da shi, 29 ga Mayu, 2023, yana mai bayyana tsarin a matsayin wanda ba zai iya dorewa ba.
A ranar Laraba, Gwamnatin Tarayya ta ce cire tallafin man fetur da kuma ’yanta tsarin musayar naira sun samar wa tarayyar Nijeriya da Naira rarar tiriliyan 15.8 a tsakanin watan Yunin 2023 da Disambar 2025.
Sai dai yayin hirar, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce duk da cire tallafin man fetur, gwamnatin Tinubu ta gaza wajen inganta rayuwar ’yan Nijeriya.
Atiku ya amince cewa tun farko ya goyi bayan cire tallafin, amma ya ce abubuwan da suka faru tun bayan cire shi sun sa ya sauya matsayarsa.
“Tun farko ban yi adawa da cire tallafin man fetur ba. Amma yanzu da aka cire shi, ina kuɗin suke?” in ji Atiku.
Ɗan takarar shugaban ƙasar ya yi alƙawarin sauya wannan manufa idan ya kayar da Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Ya ƙara da cewa: “Idan na lashe zaɓen shugaban ƙasa, zan dawo da tallafin mai. Kuma duk wanda ya sace kuɗaɗen tallafin Nijeriya dole ne ya mayar da su. Yanzu an cire tallafin, amma ina kuɗin suke? Da a ce an yi amfani da kuɗaɗen wajen inganta harkar lafiya, ilimi, magance rashin tsaro, tsaro da kuma bunƙasa matasa, da abubuwa sun fi kyau.”
Atiku ya kuma nuna shakku kan Naira tiriliyan 15 da gwamnatin Tinubu ta ce ta tara sakamakon cire tallafin, yana mai cewa rashin adalci da cin hanci tsakanin shugabannin siyasa ne manyan dalilan da suka jefa ’yan Nijeriya cikin wahala.
















