Adadin masu ɗauke da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya haura 5,000, kamar yadda bayanan gwamnati suka nuna a daren Talata, yayin da jami’an kiwon lafiya ke gargaɗin cewa ƙoƙarin daƙile cutar na fuskantar matsala wajen hana yaɗuwar wannan mummunar cuta.
Annobar Ebola ta 17 da ta ɓarke a ƙasar ta zama mafi girma a tarihin ƙasar ta fuskar yawan masu kamuwa da cutar a ƙarshen watan Yuli, yayin da adadin waɗanda suka mutu ya kai 2,378 a ƙarshen makon da ya gabata, a cewar cibiyar kula da lafiyar jama’a.

Cibiyar ta yi rajistar mutane 5,021 da suka kamu da cutar a sabon rahoton halin da ake ciki, lamarin da ya sanya wannan annobar ta zama ta biyu mafi muni a duniya ta fuskar yawan masu kamuwa da cutar da kuma mace-mace, bayan annobar Ebola da ta auku a Yammacin Afirka tsakanin 2014 zuwa 2016.
Annobar ta samo asali ne daga nau’in Ebola mai suna Bundibugyo, wanda har yanzu ba a samu allurar rigakafi ko maganin da aka amince da shi a hukumance domin yakar sa ba.
Cutar ta ƙara yaɗuwa tun bayan da aka ayyana ɓullar annobar a ranar 15 ga Mayu, yayin da ƙarancin kayan aikin kiwon lafiya, turjiya daga wasu al’umma, rashin zaman lafiya da kuma zanga-zangar ma’aikatan da ke aikin yaƙi da cutar ke kawo cikas ga ƙoƙarin gano masu ɗauke da cutar da kuma dakile yaɗuwarta.
















