Lionel Messi ya sake ɓarar da fenareti yayin da kulob ɗinsa, Inter Miami, ta sha kaye da ci 4-1 a Nashville ranar Asabar, a wata karawa tsakanin manyan ƙungiyoyi biyu na Gasar Lig ɗin Amurka (MLS).
Kafin a tafi hutun rabin lokaci ne a aka tare fenaretin Messi ɗin, wanda shi ne karo na uku a jere da ya gaza zura ƙwallo a raga daga fenareti bayan ya gaza zura fenareti a raga a wasan da ƙsarsa ta buga da Austria da Masar yayin Gasar Kofin Duniya ta 2026. Sai dai kuma, ɗan wasan gaban mai shekara 39 ya taimaka wajen ƙwallo ɗaya tilo da ƙungiyarsa ta zura a raga a wasan.
Wannan shi ne wasansa na farko tun lokacin da mahaifinsa, Jorge Messi, ya rasu ranar 8 ga watan Agusta.
A halin yanzu dai ƙungiyar Nashville ce ke saman teburin gasar lig ɗin MLS da maki 43, gaba da Inter Miami mai maki 38, wadda ke riƙe da kofin lig ɗin.
















